logo

HAUSA

Makami mai linzami na Isra’ila ya tarwatsa wani sansanin sojojin Syria

2020-11-25 13:01:30 CRI

Wani makami mai linzami da sojojin kasar Isra’ila suka harba, ya tarwatsa sansanin sojojin kasar Syria dake kudu da wajen birnin Damascus a daren jiya Talata, lamarin da ya haifar da barna mai yawa a sansanin.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kamfanin dillancin labarai na Syria SANA, ya ruwaito wata majiyar sojojin kasar na cewa, dakarun Isra’ila sun harba makamai masu linzami ne, ‘yan mintuna kafin tsakar dare, daga wani wuri dake kusa da tuddan Golan, ko da yake dai ba a tabbatar da wurin da sojojin na Isra’ila suka hara ba.

Harin shi ne na baya bayan, cikin jerin hare haren da dakarun Isra’ila ke kaiwa sansanonin dake Syria, ciki har da na mayakan dake samun goyon bayan kasar Iran.

A shekarun baya bayan nan, Isra’ila ta kaddamar da hare hare masu yawa ta sama, kan mayakan dake da alaka da kasar Iran, masu samun mafaka a Syria, baya ga wasu hare haren da ta kaiwa jerin gwanon motocin dake kaiwa kungiyar Hezbollah makamai.

Ana zargin kasar Iran ce ke taimakawa kungiyar Hezbollah, ta mayakan sa kai dake Lebanon. (Saminu)