logo

HAUSA

Ghana na fatan samar da karin sansanonin soji a dukkanin sassan kasar

2021-02-12 15:59:05 CRI

Mutumin da aka gabatar da sunan sa domin tantancewa, gabanin nadin sa a matsayin ministan ma’aikatar tsaron kasar Ghana Dominic Nitiwul, ya ce mahukuntan Ghanan na fatan samar da sansanonin sojoji a dukkanin jihohin kasar 16, a wani mataki na karfafa yaki da karuwar ayyukan ta’addanci da rashin tsaro.

Dominic Nitiwul, wanda shi ne ministan tsaron kasar mai ci, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa ‘yan kwamitin nada mukamai a majalissar dokokin kasar bayani. Ya ce a baya kasar na da irin wadannan sansanoni guda 7 lokacin da ake da jihohi 10 kacal.

Kaza lika Mr. Nitiwul, ya tabbatar da cewa ko da a yanzu ma, akwai sojoji a dukkanin jihohin kasar ta Ghana, to sai dai kuma gwamnati na fatan samar da sansanoni na dindindin, domin su ci gaba da dafawa ‘yan sanda a ayyukan wanzar da doka da oda.

Bugu da kari, ministan ya ce burin Ghana shi ne tabbatar da tsaron dukkanin sassan kasa. Kuma domin yaki da ta’addanci, an fara kafa wasu sansanonin dakarun tsaro a kan iyakokin kasar. An kuma yi nisa, wajen aiwatar da tsare tsare na samar da a kalla sansanonin soji 15, a sassan arewacin kasar don tabbatar da tsaron kasa. (Saminu)