logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Ghana ya mika takardar nadin kasa ga shugaban kasar

2021-02-03 10:39:11 CRI

Jakadan Sin dake Ghana ya mika takardar nadin kasa ga shugaban kasar_fororder_1

Ranar 1 ga wata da yamma, sabon jakadan kasar Sin dake kasar Ghana Lu Kun ya mika takardar nadin kasa ga shugaban kasar Nana Akufo-Addo, daga bisani kuma suka yi tattaunawa ta sada zumunci.

Lu Kun ya ce, tsoffin shugabannin kasashen Sin da Ghana ne suka kulla zumunci a tsakanin kasashen biyu, kuma zumunci zai dore har abada. A cikin 'yan shekarun nan, kasashen biyu sun samu sakamako mai kyau a hadin gwiwar siyasa, tattalin arziki da kasuwanci, al'adu, ilimi, kiwon lafiya, da aikin soja da dai sauransu dake tsakaninsu.

A cewar Lu Kun, yana matukar farin cikin zama jakadan kasar Sin a Ghana, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da bangaren Ghana don ciyar da alakar kasashen biyu zuwa gaba.

Jakadan Sin dake Ghana ya mika takardar nadin kasa ga shugaban kasar_fororder_2

A jawabinsa, shugaba Addo, ya yi maraba da jakada Lu, kan sabon mukamin da ya samu, ya kuma jaddada cewa, kasarsa na mutunta manufar Sin daya tak, wadda ita ce babbar manufar diplomasiyya ta Ghana. Haka kuma kasar Ghana, za ta ci gaba da martaba wannan manufa. Kawancen Ghana da Sin na da dadadden tarihi, kuma Ghana na mai da hankali sosai ga raya dangantakarta da Sin. A cikin 'yan shekarun nan, hakikanin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu ya samu karin nasarori. A cewar shugaban, yana gode wa kasar Sin matuka bisa gagarumin goyon bayan da take baiwa bunkasuwar tattalin arzikin Ghana, musamman ma wajen yaki da annobar COVID-19, kuma kasarsa a shirye take ta ci gaba da bunkasa dangantakar dake tsakanin ta da Sin. Ya ce yana fatan karin kamfanonin kasar Sin, za su yi amfani da wannan dama, ta bude sakatariyar yankin cinikayya cikin ‘yanci na Afirka, don kara saka jari a Ghana da ma nahiyar Afirka baki daya. (Bilkisu)