logo

HAUSA

Iran ta ce bai dace ta tattauna da EU da Amurka a yanzu ba

2021-03-01 13:00:56 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Saeed Khatibzadeh ya bayyana cewa, bai dace kasarsa ta tattauna da kungiyar tarayyar Turai da Amurka a wannan lokaci ba, bisa la’akari da matsayi da matakai na baya-bayan da Amurka da wasu kasashen Turai guda uku suka dauka.

Ya ce, Jamhuriyar Islama ta Iran tana ganin yanzu ba shi ne lokacin da ya dace ta gudanar da tattaunar da mai shiga tsakani na EU game da yarjejeniyar nukiliyar kasar(JCPOA) ya shirya ba.

A makon da ya gabata ne, kungiyar tarayyar Turai ta yi tayin halartar tattaunawa tsakanin Iran da sauran bangarorin da yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma a shekarar 2015 ya shafa, inda Amurka za ta halarci taron a matsayin bakuwa.

An ruwaito Khatibzadeh na cewa, har yanzu Amurka ba ta sauya matsayi da ma halayyarta ba. (Ibrahim)

Ibrahim