Shugaban Amurka ya gargadi Iran da ta yi taka tsantsa
2021-02-27 15:48:27 CRI
Shugaban Amurka Joe Biden, ya gargadi Iran da ta yi taka tsantsa, bayan hari ta sama da Amurkar ta kai Syria.
Joe Bidan ya bayyana haka ne jiya, lokacin da aka tambaye shi game da sakon da yake son aikewa Iran dangane da harin.
Ma’aikatar harkokin wajen Iran, ta yi tir da harin na dakarun Amurka a gabashin Syria, tana mai bayyana shi a matsayin wanda ya keta doka.
Bisa labarin da aka wallafa a shafin website na ma’aikatar, kakakin ma’aikatar Saeed Khatibzadeh, ya kira harin da take hakkokin bil adama da dokokin kasa da kasa a fili.
A cewarsa, cikin ‘yan shekarun da suka gabata, dakarun Amurka sun shiga Syria ba bisa ka’ida ba, inda suka mamaye wasu yankunan kasar, yana mai cewa, Amurka ta sace albarkatun Syria, kamar man fetur, wadanda suka kasance mallakin al’ummar kasar.
Ya ce matakin na Amurka, zai kara ta’azzara rikicin sojoji da tashin hankali a yankin. (Fa’iza Mustapha)