logo

HAUSA

Shugaban CMG ya yi kira ga kafafen yada labaran yamma su gyara kurakurensu na jirkita gaskiyar labaran da suka shafi kasasr Sin

2021-01-02 16:26:13 CMG

Shugaban CMG ya yi kira ga kafafen yada labaran yamma su gyara kurakurensu na jirkita gaskiyar labaran da suka shafi kasasr Sin_fororder_A

Shugaban babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, Mista Shen Haixiong, ya gabatar da jawabin murnar sabuwar shekarar 2021, inda ya sake kira ga wasu kafafen yada labaran kasashen yammacin duniya, su gyara kurakuren da suka tafka na nuna bambanci gami da jirkita gaskiya kan rahotannin da suka shafi kasar Sin. Ya kuma bukaci su sauke nauyin dake wuyansu yadda ya kamata ta hanyar nunawa da inganta kwarewa ta fuskar watsa labarai masu inganci. Shen ya jaddada cewa, ra’ayi riga, kowa da irin tasa, amma kuma, gaskiya daya ce. Don haka yayin da aka shiga sabuwar shekarar, ya kamata a rage yada jita-jita a fadin duniya.

A jawabin da ya wallafa a shafukan sada zumunta na kasa da kasa, Mista Shen ya jaddada cewa, ya dade da gane cewa, fadar gaskiya ita ce rayuwar kafofin watsa labarai. Kuma rahotanni masu inganci da gaskiya su ke nuna kwarewar kafofin watsa labarai. Amma abun takaici shi ne, yadda wasu kafafen yada labarai suka jirkita gaskiya da nuna bambanci kan rahotannin da suka ruwaito dangane da kasar Sin. Ko a fannin dakile annobar COVID-19, ko kuma batutuwan da suka shafi Hong Kong da Xinjiang, duk akwai labaran bogi da ake yadawa har ma akwai wadanda suka wuce gona da iri.

Mista Shen ya ce, dangane da rade-radin dake bazuwa, CMG ya maida martani ba tare da bata lokaci ba don karyata su. Ya kuma ruwaito wani karin magana daga nahiyar Turai dake cewa “masu tabbatar da adalci sun fi samun yawan abokai”. Wato a shekara ta 2021, CMG zai ci gaba da sauke nauyin dake wuyansa a matsayin muhimmiyar kafar yada labarai a duniya, da tsage gaskiya komai dacinta da tabbatar da adalci, a kokarin watsa sahihan labarai ga duk duniya domin cin gajiyar wayewar kan bil adama.(Murtala Zhang)