logo

HAUSA

Jawabin Shugaban CMG Na Murnar Sabuwar Shekarar 2021 Ga Masu Sauraro Da Masu Kallo

2021-01-01 15:15:56 CRI

Jawabin Shugaban CMG Na Murnar Sabuwar Shekarar 2021 Ga Masu Sauraro Da Masu Kallo_fororder_慎海雄

Yau 1 ga watan Janairun shekarar 2021, shugaban babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG, Mista Shen Haixiong, ya mika gaisuwa da fatan alheri ga masu sauraro da masu kallo, ta gidan rediyon kasar Sin na CRI da yanar gizo ta Intanet. Ga dai cikakken jawabin taya murnar sabuwar shekarar da shugaban na CMG ya gabatar.

Abokai da aminai, barkanku da war haka.

Yayin da muka shiga sabuwar shekarar 2021, wadda ita ce shekarar dabbar Sa bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Sa na taka muhimmiyar rawa a ayyukan gona. A ganin Sinawa, Sa dabba ce mai jure wahala, ban da haka kuma, shanu suna da matukar karfi. Ina so in yi amfani da wannan dama wajen isar da gaisuwa ta gare ku daga nan birnin Beijing, tare da fatan za ku kasance cikin koshin lafiya kamar shanu.

Shekarar 2020 da muka yi ban kwana da ita, ta kasance ta musamman, inda duk duniya ta fuskanci kalubalen da ba a taba gani ba. Annobar COVID-19 da ta bulla ba zato, ta jefa daukacin bil Adama cikin mawuyacin hali. Amma aikin yaki da annobar ya samu gagarumar nasara a kasar Sin, karkashin jagorancin shugaban kasar Xi Jinping da ma namijin kokarin daukacin al’ummar kasar. Har ila yau, kasar Sin, ta kasance kasa daya tak da ta samu karuwar tattalin arziki a duk duniya.

Har yanzu, cutar COVID-19 na ci gaba da yaduwa a kasashen duniya da dama. Don haka, muna taya su juyayi, tare da fatan ganin bayan cutar cikin hanzari, da kasancewar kowa cikin koshin lafiya.

A matsayin ‘yan jarida, watsa sahihan labarai shi ne aikinmu. A farkon bullar annobar COVID-19, ba tare da wani jinkiri ba, abokan aiki na fiye da 2000 sun tafi yankin da cutar ta fi tsanani a kasar Sin. Ta hanyar bayar da rahotanni daga dakunan kwantar da wadanda suka kamu da cutar, da shirin bidiyo na Documentary mai taken “Yaki da annoba cikin hadin kai” da sauransu, sun nuna wa duniya yadda Sin ta yi kokarin yaki da cutar a kan kari.

Ban da wannan kuma, mun tsara wani shirin talibijin na musamman mai suna “COVID-19 Frontline”, inda muka gayyaci likitoci daga wasu kasashe, don tattaunawa da takwarorinsu na kasar Sin dangane da aikin yaki da cutar. Haka zalika, mun samu damar tattaunawa da babban editan mujallar lafiya ta The Lancet, Mista Richard Horton, da Mista Peter Forster na Jami’ar Cambridge, wanda ya kasance marubucin rahoto na farko dangane da sauyin kwayoyin cutar COVID-19, da dai sauran masana, a kokarin kawar da jita-jitar da aka yada kan cutar, bisa dogaro da sahihan bayanai da ma ilmin kimiyya.   

A cikin shekarar 2020 da ta wuce, mun gano kaunar da ke tsakanin mutane. Kamar yadda Zhang Zai, masanin falsafa na daular Beisong ta Sin ya taba fada shekaru fiye da 900 da suka gabata, fatara da bakin ciki za su taimaka wajen kara karfin zukatan jama’a da ma samun nasara. Ban da wannan, wahalhalu sun ba mu damar gano kauna da kulawar dake akwai a tsakaninmu, da babbar ma’anar raya makomar bil Adama ta bai daya. Yayin da muke tinkarar cutar, mun kara fahimtar cewa, ba za a iya samun nasara a kan cututtuka da sauran kalubale ba, har sai mu bil Adama mu hada gwiwa.

Duk da cewa annobar COVID-19 ta kawo cikas ga mu’amalarmu fuska da fuska, a daya hannun ta sa zukatanmu sun kara kusantar juna. A cikin shekarar da ta gabata, ni da takwarori na na gidajen rediyo da talibijin na Rasha, da Jaridar Rasha, BBC, CNN, AP, Reuters, AFP, NHK, gidan rediyo da talibijin na Italiya, da kawancen rediyon kasashen Turai, da ma jakadun kasashen waje da ke Sin, mun aikewa juna wasiku kusan 300, domin sada zumunci da jaddada nauyin da ke wuyanmu, da ma karfafa ra’ayinmu na bai daya. Bugu da kari kuma, CMG ya tattauna da kafofin watsa labarai fiye da 100 daga Turai da Latin Amurka, kan aikin yaki da cutar, ta hanyar shirin tattaunawa ta Intanet, baya ga kafa tsarin hadin gwiwa da dimbin kafofin watsa labarai domin daukar shirye-shiryen bidiyo kamar na “Dukiyoyi mafiya daraja na Sin” da dai sauransu, wadanda suka burge jama’a sosai.

Ban da annobar, talauci, matsala ce da ta addabi bil Adama. Kamar yadda Shugaba Xi Jinping ya bayyana, kawar da talauci, buri ne da bil Adama ke kokarin cimmawa tun fil azal, kana neman kyautata rayuwa, babban hakki ne dake kan al’ummun kasa da kasa. A cikin shekarar da ta wuce, kasar Sin ta samu nasarar fatattakar fatara baki daya. Wato bayan ta yi gwagwarmaya har ta tsawon shekaru 8, yanzu Sinawa kimanin miliyan 100 sun fita daga kangin talauci, lamarin da ya zama tamkar abin al’ajabi a tarihin bil Adama a fagen yaki da talauci.

Domin tunawa da wannan muhimmin batu, mun fitar da shirin bidiyo na Documentary mai taken “Yadda Sin ta kokarta wajen yaki da talauci” wanda aka watsa shi cikin harsuna da dama, da tsara shirin musamman mai suna “Yaki da fatara—shawara ga duk duniya ta shekarar 2020” da dai sauransu. Muna fatan kasashe da jama’a masu fama da talauci za su samu fasahohin da za su yi koyi da su daga shirye-shiryenmu.

Yayin da muke sauke nauyin da ke wuyanmu a matsayin kafar watsa labarai, muna ci gaba da raya kafarmu daga dukkan fannoni bisa tushen amfani da yanar gizo, a kokarin cimma burinmu na zama babbar kafar watsa labarai ta ajin farko mai sabon salo a duniya. Ta hanyar amfani da fasahohin 5G+4K da ma 8K+AI, mun samu nasarar watsa shirin bidiyo na kai tsaye kan yadda na’urar binciken duniyar wata kirar Chang’e-5 ta kasar Sin ke debo tabo daga duniyar wata, da yadda jirgin ruwan Fendouzhe ya yi nutson zurfin da ya kai sama da mitoci 10,000 a cikin teku. A wurin biki karo na uku, na baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin, mun tsara hanyar sayen hajoji masu inganci bisa amfani da shirin bidiyo na kai tsaye ta Intanet, wanda ya taimakawa dimbin hajojin Turai samun kasuwa a kasar Sin.

Ko da yaushe ina ganin cewa, tabbatar da sahihancin labari shi ne ran kafar watsa labarai. Sahihan labarai daga tushe na shaida nauyin da ke wuyan kafofin watsa labarai da ma nagartarsu. Amma abin takaici shi ne, yadda wasu kafofin watsa labarai ke nuna son zuciya da yada jita-jita kan labaran da suka danganci kasar Sin. Idan aka duba fannin shawo kan cutar COVID-19, da labaran da suka shafi yankin Hong Kong da jihar Xinjiang, sun yi ta tafka kura kurai. Daga bangarenmu, mun maryar da martani nan take, tare da bayyana asalin labaran. Duk da cewa ana iya samun ra’ayoyi daban daban kan wani batu, gaskiya dai daya ce. A cikin wannan sabuwar shekarar da muka shiga, ‘yan jarida a duk fadin duniya na da alhakin rage yawan jita-jita.

Masu iya magana na Turai na cewa, “masu adalci sun fi samun yawan abokai”. A bana, CMG zai ci gaba da sauke nauyin da ke wuyansa, na tsage gaskiya komai dacinta da tabbatar da adalci, a kokarin watsa sahihan labarai ga duk duniya domin cin gajiyar wayewar kan bil adama.

A shekarar nan ta 2021 ake cika shekaru 100 da kafuwar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin. Daga ‘yan jam’iyya 13 a farkon kafuwarta, har zuwa ‘yan jam’iyyar fiye da miliyan 90 a yanzu, ko mene ne sirrin farfadowar kasar Sin a karkashin jagoranci jam’iyyar? Mene ne dalilin da ya sa Sinawa kimanin biliyan 1.4 ke mara mata baya? A bana, za mu mai da hankali kan wannan batu. Sa’an nan za mu ci gaba da aiki tukuru don kawo muku dadadan shirye-shirye kan Sin da ma duniya baki daya.

A karshe dai, ina sake yi muku fatan alheri a wannan sabuwar shekarar Sa ta kasar Sin.(Kande Gao daga sashen Hausa na CRI)