logo

HAUSA

CMG ta kaddamar da shirin tallata hajojin lardin Hubei na shekarar 2021

2021-01-08 20:36:35 CRI

A yau Juma’a 8 ga watan Janairu ne, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya kaddamar da wani shirin musamman mai lakabin "Brand Power Project" na shekarar 2021, domin taimakawa lardin Hubei na kasar Sin, da damar yayata hajojin sa kai tsaye a biranen Beijing da Wuhan.

Karkashin wannan shiri, helkwatar CMG za ta ci gaba da samar da damammakin tallace tallace, da kimar su za ta kai kudin kasar yuan miliyan 500 kyauta, don farfado da tattalin arzikin lardin na Hubei, da tsare tsaren karfafa gwiwar masu sayan hajoji, ta yadda za su rungumi kayayyakin da aka samar daga lardin na Hubei.

Kaza lika CMG zai gudanar da shirye shirye 5 kai tsaye, domin tallata hajojin lardin, duka dai da nufin yayata hajojin dake fitowa daga Hubei, da kuma fadada cinikin su.   (Saminu)