logo

HAUSA

Gasar Wasannin Olympic Ta Beijing Ta Lokacin Sanyi Ta Kwantar Da Hankalin Kasa Da Kasa

2021-02-03 19:52:10 CRI

Yau shekaru 6 da suka wuce, Thomas Bach, shugaban kwamitin harkokin wasannin Olympic na duniya ya sanar da cewa, Beijing ta samu bakuncin shirya gasar wasannin Olympic ta shekarar 2022 ta lokacin sanyi, tare da nuna cewa, hankalin kowa da kowa ya kwanta, saboda Beijing ta samu bakuncin shirya gasar. Kamar yadda ya yi zato a baya, yanzu ana share fagen gasar ba tare da wata matsala ba a Beijing.

Yau 4 ga wata, ya rage shekara guda kacal a bude gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing ta lokacin sanyi. Kwanan baya, yayin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi hira da shugaba Bach ta wayar tarho, ya nuna imaninsa da cewa, sakamakon goyon bayan da sassa daban daban suke bayarwa ya sa, tabbas kasar Sin za ta kammala dukkan ayyukan share fagen gasar daidai lokacin da aka tsara, za ta shirya gasar cikin cikakkiyar nasara.

Yayin da ake yaki da annobar COVID-19, kasar Sin tana daukar hakinanan matakai wajen cika alkawarin da ta yi, lamarin da ya karfafa gwiwar wasan Olympic na kasa da kasa sosai duk da kasancewar rashin tabbas da ake fuskanta. Yadda kasar Sin za ta shirya gasar wasannin Oylmpic ta Beijing ta lokacin sanyi daidai lokacin da aka tsara, ya karfafa gwiwar mutanen kasar miliyan 300, su yi wasanni kan kankara da dusar kankara, kana kuma zai ba da gudummawa ga ci gaban duniya.

Babu tantama a shekarar 2022, kasashen dunya za su gane wa idanunsu yadda kasar Sin za ta cika alkawarinta, za ta shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ta lokacin sanyi cikin cikakkiyar nasara. Kowa da kowa zai ji dadin wata kasaitacciyar gasa mai kayatarwa. Har ila yau, birnin na Beijing, wanda shi ne birni daya tilo a duniya da ya shirya gasar wasannin Olympic ta lokacin zafi da ta lokacin sanyi, zai ba da nasa gudummawa wajen raya wasan Olympic na duniya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan