logo

HAUSA

Xi Jinping yana mai da hankali kan yadda ake amfani da fasahohin zamani wajen shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi

2021-02-03 13:57:48 CRI

Yanzu shekara guda ya rage a kaddamar da gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekara ta 2022, gami da ta nakasassu. Shugaban kasar Sin Xi Jinping yana maida hankali sosai da sosai kan gudanar da wannan gagarumar gasa ta kasa da kasa, inda ya sha jaddada cewa, ya dace a yi amfani da kimiyya da fasaha na zamani don gudanar da gasar, tare da yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha wajen bunkasa wasannin motsa jiki na lokacin hunturu na kasar Sin.

“Ni da al’ummun kasar Sin, muna maraba da abokai daga sassan duniya, mu hadu a Beijing a shekara ta 2022. Maraba da zuwanku, maraba da zuwan abokanmu.”

A ranar 25 ga watan Fabrairun shekara ta 2018, a yayin bikin rufe gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi a birnin Pyeongchang na kasar Koriya ta Kudu, shugaba Xi ya gayyaci daukacin duniya da su halarci gasar Olympics ta lokacin hunturu ta shekara ta 2022 da za a gudanar a Beijing.

Gina dakunan wasa da inganta wasu muhimman ababen more rayuwar al’umma na da matukar muhimmanci ga cimma nasarar gudanar da gasar Olympics. Ta yaya za a tabbatar da ingancin dakunan wasan da aka gina a wasu yankunan da za a gudanar da gasar Olympics ta Beijing? Tun shekaru hudu da suka wuce, lokacin da yake gudanar da bincike kan aikin shirya gasar, Xi Jinping ya ce:

“Wani muhimmin aiki na gudanar da gasar wasan Olympics a lokacin hunturu shi ne aikin gina dakunan wasa. Ya kamata dakunan da za mu gina, su bayyana salon musamman da muke da shi, wanda ke kunshe da kimiyya da fasaha, da hikima, kuma ba tare da gurbata muhalli ba. Ya dace mu kara amfani da fasahohin zamani don gina dakunan wasanni daban-daban.”

Muna iya ganin cewa, wasu manyan dakuna gami da filayen wasanni da aka gina don gudanar da gasar wasan Olympics ta lokacin sanyi a Beijing sun kunshi abubuwa da dama na fasahohin zamani, ciki har da babban filin wasan zamiyar kankara da dakin wasan gudun keke a kan kankara da sauransu. Duk da cewa ana fuskantar yaduwar annobar COVID-19, amma yadda aka kammala aikin gine-ginen dakuna da filayen wasanni baki daya, shekara guda kafin lokacin fara gasar, gaskiya ya gamsar da kowa da kowa.

A shekara ta 2017, shugaba Xi ya nuna cewa, ya kamata kasar Sin ta kara yayata wasannin motsa jiki na kankara a tsakanin jama’a, da inganta kwarewar ‘yan wasanni a wannan fanni, inda ya ce:

“Wasannin motsa jiki na kankara ba su cika samun karbuwa a kasarmu ba, don haka, kamata ya yi mu kara yayata su ga jama’a da inganta kwarewar ‘yan wasannin ta hanyar gudanar da gasar Olympics ta lokacin sanyi. Ya kamata mu kara kyautata ayyukanmu na raya wasannin motsa jiki na kankara. Kuna da kuzari, yara ku yi kokari!”

A ranar 18 ga watan Janairun bana, shugaba Xi ya ziyarci babbar cibiyar wasan zamiyar kankara ta kasar Sin, inda ya karfafawa ‘yan wasanni gwiwa. Rahotanni na cewa, saboda yadda aka fara amfani da wasu fasahohin zamani, ciki har da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI, an kara inganta kwarewar ‘yan wasannin kankara. Game da wannan batu, shugaba Xi ya jaddada cewa, inganta kwarewar ‘yan wasa na zamani, yana bukatar karfi da kuma fasaha, wato kamata ya yi a yi kirkire-kirkire a bangaren kimiyya da fasaha don raya harkokin motsa jiki. Shugaba Xi ya ce:

“Wadanne matakai ya kamata mu dauka wajen bunkasa harkokin wasanninmu na motsa jiki? Abu daya ne da hanyar da kasarmu take bi wajen samun karfi da ci gaba, wato mu dogara kan ayyukan kirkire-kirkire da kimiyya da fasaha. A wani bangaren, ya kamata mu yi kirkire-kirkire bisa karfin kanmu. A dayan bangaren kuma, mu koyi fasahohin zamani daga kasashen duniya daban-daban, da nazarin yadda suke horas da ‘yan wasansu, ta yadda kwarewamu za ta inganta”. (Murtala Zhang)