logo

HAUSA

Xi ya ce Sin za ta tabbatar da nasarar wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing

2021-01-26 10:05:23 CRI

Xi ya ce Sin za ta tabbatar da nasarar wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing_fororder_20210126-Ahmad 1-hoto

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a jiya Litinin cewa, ya yi amanna bangaren kasar Sin ta hanyar cikakken goyon bayan dukkan bangarori, za ta cimma nasarar kammala dukkan shirye shirye kamar yadda aka tsara, domin tabbatar da nasarar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing.

Xi ya ce, bangaren kasar Sin yana matukar farin ciki bisa irin goyon bayan da hukumar shirya wasannin Olympics ta kasa da kasa wato IOC take baiwa fannin wasanni na kasar Sin, kuma kasar za ta ci gaba da goyon bayan ayyukan hukumar ta IOC, ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta bi sahun hukumar IOC da sauran kasashen duniya domin tabbatar da samun nasarar karbar bakuncin gasar Tokyo Olympics da ta Beijing Winter Olympics, kuma za ta bada gudunmawar farko na samun nasarar kasa da kasa a yaki da annobar COVID-19, da farfadowar tattalin arzikin duniya, da kuma kiyaye rayuka da lafiyar al’ummun dukkan kasashen duniya.

Kasar Sin tana daukar batun shirye shiryen gasar Beijing Winter Olympics a matsayin wata dama ce ta daga matsayi da ci gaban wasannin kankara, in ji shugaba Xi, ya kara da cewa, Beijing, shi ne birni daya tilo a duniya da ya karbi bakuncin gasar wasannin motsa jiki ta lokacin zafi da kuma ta lokacin hunturu, zai bada gudunmawa ta musamman ga fagen wasannin Olympics na kasa da kasa.

A nasa bangaren, shugaban hukumar IOC Thomas Bach, ya ce karkashin shugabanci mai karfi na shugaba Xi, kasar Sin ta samu manyan nasarori wajen kawar da annobar COVID-19, ita ce kasar dake sahun gaba wajen farfadowar tattalin arziki a duniya, kana ta zama babbar jagorar farfadowar tattalin arzikin duniya.

Ya ce, IOC tana goyon bayan tunanin kasar Sin na shirin karbar bakuncin gasar ta hanya makamashi mai tsafta, da shigar da kowane bangare, da bude kofa, da karbar bakuncin gasar ta Olympics ta lokacin hunturu bisa tsari mai inganci, kuma a shirye hukumar take ta yi aiki tare da kasar Sin domin cimma nasara, da kafa tarihi mai ban mamaki, da gudanar da gasar cikin yanayi mai kyau, wanda ba kawai zai tabbatar da cimma nasarar burin daga matsayin wasannin kankara a tsakanin Sinawa miliyan 300 ba ne, har ma zai daga matsayin ci gaban wasannin Olympics na kasa da kasa. (Ahmad Fagam)