logo

HAUSA

Na’urorin zamani na taimakawa ayyukan shirya gasar Olympics ta birnin Beijing

2021-01-28 20:01:49 CRI

Na’urorin zamani na taimakawa ayyukan shirya gasar Olympics ta birnin Beijing_fororder_6a4f6b89814f45009fa3cb5964b0fe32

Na’urorin zamani da ake samarwa domin gudanar da ayyuka daban daban, na taimakawa ayyukan shirya gasar Olympics ta lokacin hunturu wadda birnin Beijing zai karbi bakunci.

Masu bibiyar shirye shiryen da ake gudanarwa gabanin gasar ta shekarar 2022, na bayyana tasirin irin na’urori masu kunshe da fasahohi daban daban da ake kerawa a sassan kasar Sin, don tallafawa nasarar wannan gasa ta Olympic da ta ajin nakasassu dake tafe. Karkashin wannan manufi, an kafa wasu dakunan gwaje gwaje, da shirye shirye a wasu jami’oi da filayen wasanni dake sassan kasar.

A yayin wannan gasa ta Olympics ta lokacin hunturun shekarar badi, ‘yan wasan motsa jiki daga sassan duniya daban daban, ba wai kawai za su fafata neman lambobin yabo ba ne da nuna kwarewa kadai, a hannu guda za su yi takara da fasahohin da aka tanada, domin taimakawa samun horo da kuma gasa.

Kayan fasahohin na makalawa a jiki da kayan sawa na musamman

Wani ci gaba da aka samu shi ne, samar da na’ura ta sanyawa a jiki mai auna bugun jini a zuciya yayin da mutum ke tuki a kan keke, na’urar na iya auna yawan iskar oxygen da yake shaka, da sinadaran jini, da karfin tukin keken sa, da sauran yanayi na cikin jiki dake bayyana a allon dake gaban wannan keke.

Liu Junyi, shi ne daraktan dakin gwaji na gasar Olympics dake jami’ar Northeast Normal dake birnin Changchun, fadar mulkin lardin Jilin na arewa maso gabashin kasar Sin. Jami’in ya gabatar da wannan na’ura dake kafe a jikin keken gwaji da aka kera.

Daraktan ya ce akwai kuma wani inji da ake iya amfani da shi domin wasan kankara na zamiya da ake kira da “alpine skiing”, da wasan zamiya kan allon kankara, yana kuma dauke da tsarin yin jinyar kwanjin jikin dan wasa, wanda aka kera musamman domin yan wasan kankara. Daraktan ya ce dakin gwajin nasa tamkar asibiti ne, da wurin kara yawan makamashi ga yan wasa.

An kafa wannan cibiyar gwajin ne a shekarar 2015, a jami’ar ta Northeast Normal, tana kuma da sassan aikin gwaji guda 6, da nau’oin dakunan gwaji 24, da kuma na’urorin gwaje-gwaje sama da 500.

Cibiyar gwajin na da wurin auna yanayin motsa jiki, da na auna dabarun motsa jiki, da dabarun nuna kwarewa, da wurin jinya, da sauran wasu hidimomi ga ‘yan wasa sama da 1,000 dake kasar Sin.

A wata cibiyar ta gwajin fasahohi dake birnin Beijing kuwa, dalibi Cao Hongqing dake aiki a fannin amfani da na’urori masu sarrafa kan su, na aiki kan wani karfe mai tsayin mita 12, bayan ta sanya wata na’ura mai aiki da jin motsin mutum. Da taimakon wasu allunan zamiyar kankara biyu, nan take ya fara wasan zamiya kan allon lantarki dake gaban sa.

Cao ya ce "A kan wannan allon kadai nake yin wasan zamiya. Akwai wahalar yi a nan, amma za ka ji kamar kana yin zamiyar a zahiri,". Saurin zamiyar da mutum kan iya yi a kan wannan teburi na iya kaiwa kilomita 100 duk sa’a. Na’urori dake aiki da jin motsi guda 17 da ake sanyawa a gabobin dan wasa, na iya gane yanayin motsin jikin sa da tafiyar sa, tare da taimakawa mai horaswa gane kwazon dan wasan.

Yanzu dai haka gasar Olympic ta birnin Beijing na karatowa, muna kuma fatan sakamakon binciken mu zai inganta matakin horon ‘yan wasa," a cewar Liu Xiangdong, shugaban cibiyar bincike game da kwaikwayon bil Adama, a fannin wasan zamiyar kankara, kuma shaihun malami a jami’ar BIT.

Amfanin na’urorin zamani a wuraren wasanni

A baya bayan nan ne aka kammala sashen samar da kankara a zauren wasan zamiya na “Oval” wanda kuma ake kira da zauren "Ice Ribbon," bayan shafe kwanaki 60, da haka kuma, aka kai matsayin fara gwajin wasannin kankara a wannan zaure.

A wannan zaure akwai matakai daban daban na tudun kankara, da suka kai milimita kusan 4, yayin da banbancin makin sanyi a zauren ba ya wuce 0.5 kan ma’aunin Celsius, wanda hakan ke baiwa ‘yan wasa damar yin horo cikin mafi kyawun yanayi.

Zauren "Ice Ribbon" shi ne irin sa na farko a duniya, wanda ke aiki da iska nau’in carbon dioxide don sanyaya fasahar samar da kankara, fasahar da a yanzu ita ce mafi dacewa wajen kare muhalli, yayin da ake ci gaba da samar da kankara, ba tare da fitar da iskar carbon mai gurbata muhalli ba, kana ga batun samun biyan bukatar kankara maras yankewa.

Tsawon kwanaki, Liu Ming, wanda farfesa ne a tsangayar “Optics and Photonics” dake cibiyar BIT ta birnin Beijing, shi ne ke jagorantar tawagar dake yin gwajin motsin jikin ‘yan wasa, tare da bincike game da alakar hakan da kayan da ‘yan wasan ke aiki da su, a wani zauren samun horon motsa jiki dake nan birnin Beijing.

Liu na kallon allon laturori mai fasahar 4K, inda yake lura da sakamakon gwajin da ake yi kan wasan zamiya. Liu na sarrafa na’ura mai kwakwalwa don tattarawa da nazarin dukkanin motsin da ake yi, ta wata na’urar da ake iya zuko hotunan dake fitowa kan ta, tare da kyamara mai karfin fitar da kyawawan hotuna dake kafe a zauren motsa jiki.

Liu Ming ya ce "Amfanin wannan tsarin aiki na mu shi ne, tattara alkaluman motsin masu motsa jiki, ta hanyar ci gaba da zuko hotuna da motsin dan wasa, sannan a yi nazarin dukkanin motsin don gano fasaha mafi dacewa, ta kyautata motsin, wanda hakan zai iya taimakawa ‘yan wasan da masu horas da su, iya gano dabarun kimiyya na ba da karin horo. Tsarin ya kunshi amfani da kyamarori 2 dake da karfin fitar da hotuna har Pixels miliyan 25 a allo guda, tare da tattaro karfin nuna hoto har 160 a mizanin fps, wanda ake amfani da su wajen awon motsin dan wasa ta fannoni daban daban.

Kirkire kirkire domin sufuri tsakanin birane daban daban

A gabar da ake iya amfani da fasahar 5G, da damar yin amfani da cajojin na’ura marasa amfani da waya, da hasken kyamarori na fasahar zamani, ana iya bayyana layin dogo mai saurin tafiya tsakanin birnin Beijing zuwa Zhangjiakou, a matsayin ci gaban baya bayan nan da Sin ta samu a fannin bunkasa harkar sufurin jiragen kasa, tun daga kera kayan aiki zuwa samar da sabbin kayan amfanin yau da kullum, ya zuwa sabbin fasahohin kwaikwayon tunanin bil Adama.

Hidimar sufurin jiragen kasa, mai gudun kilomita 350 duk sa’a, kan wannan layin dogo, ta rage lokacin sufuri tsakanin biranen biyu daga sa’oi 3 zuwa mintuna 47 kacal.

A karshen watan Disambar 2020, Shen Xue, tsohuwar zakarar wasan zamiyar kankara, ta amsa gayyatar da aka yi mata, ta gwada amfani da wata safar hannu ta lantarki mai lakabin RMB. Bayan sayen tikiti da kudin na’ura, ta yi mafani da safar kan dandamalin na’ura da aka tanada, domin wucewa hanyar shiga tashar jirgin kasa dake hada wadannan birane.

Kaddamar da wannan safa ta RMB da ake sanyawa a hannu, ya zama wani muhimmin mataki na ci gaba da aka cimma a birnin Beijing, a fannin gwada wannan fasaha ta safar na’urar RMB, a wuraren da za a gudanar da gasar Olympics ta lokacin hunturu dake tafe.

Wannan safa na kunshe da fasahar dukkanin abubuwan da dan wasa zai bukata yayin tafiya, kana za a yi cikakken amfani da ita a gasar Olympics ta lokacin hunturu a nan gaba. An yi amannar cewa, za ta samarwa masu zuwa yankunan gudanar da gasar cikin ‘yan wasa, da masu horaswa, da ‘yan kallo, damar biyan kudin zirga zirga cikin sauki.