logo

HAUSA

Wang Qishan ya gana da wakilan Amurka dake halartar tattaunawar tsakanin jagororin kasashen biyu a fannin masana’antu da kasuwanci da tsoffin manyan kusoshinsu karo na 12

2021-01-29 14:57:44 CRI

Yau Juma’a, mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan ya gana da wakilan Amurka dake halartar tattaunawar tsakanin jagororin kasashen biyu a fannin masana’antu da kasuwanci da tsoffin kusoshinsu karo na 12 ta kafar bidiyo a nan birnin Beijing.

Wang ya bayyana cewa, dangantakar Sin da Amurka na shafar zaman lafiya da wadata na duniya. A cikin shekaru sama da 40 da suka gabata bayan kulla dangantakar diplomasiya tsakanin kasashen biyu, Sin da Amurka sun taimakawa juna da amfanawa juna da cin moriya tare. Shekaru 50 da suka gabata bayan da dakta Henry Alfred Kissinger ya ziyarci kasar Sin, duk da cewa kasashen biyu suka samu sabani a tsakaninsu duba da cewa akwai bambanci a tsakaninsu ta fannonin tsare-tsaren zamantakewar al’umma da al’adu da ra’ayoyi da ci gaba, amma sun ci gajiyar hadin gwiwarsu. Sai dai, duk da takara a fannoni daban-daban a nan gaba, kasashen suna da muradu iri daya. A don haka, ya kamata su mutunta juna a maimakon yin jayayya tare da nacewa ga hadin kai da cin moriya tare, kuma ita ce hanya daya tilo ta raya dangantakar kasashen biyu yadda ya kamata.

Wakilan Amurka na nuna cewa, ya kamata kasashen biyu sun bi hanya mafi dacewa don hadin kansu nan gaba, ta yadda za a ba da tabbaci ga bunkasuwar dangantakarsu yadda ya kamata. Sassan masana’antu da kusuwanci na Amurka za su yi kokarin ingiza shawarwari da mu’ammala tsakanin sabuwar gwamnatin Amurka da kasar Sin. (Amina Xu)