logo

HAUSA

Hukumar kula da hada hadar hannayen jari ta kasar Sin za ta tsaurara dokoki da dakile fadawa hadurran kasuwa

2021-01-29 12:19:54 CRI

Hukumar kula da hada hadar hannayen jari ta kasar Sin, ta sha alwashin tsaurara dokoki, da dakile fadawa hadurran kasuwa a shekarar nan ta 2021.

Hukumar ta sha alwashin ne, yayin wani taron nazarin ayyukan ta da ya gudana a jiya Alhamis, tana mai cewa, za ta tabbatar da daidaituwar harkokin da suka shafi gabatar da hannayen jari, da na sake sayen su, da aiwatar da matakan inganta farashin hajoji da cinikayyar su.

Yayin da hukumar ke aikin lura da bayanai masu nasaba da hada hadar kamfanonin da suke gudanar da kasuwancin hannayen jari, a hannu guda kuma, za ta fitar da wasu tsauraran ka’idoji na dakile kaucewa ka’ida yayin da kamfanoni ke kokarin fadada jarin su.

Hukumar ta kara da cewa, za ta kara azama wajen daidaita tsarin bin ka’idojin kasuwa tsakanin kamfanoni dake gabatarwa al’umma hannayen jari, da aiwatar da matakin cire wadanda ba sa cika sharudda. (Saminu)