logo

HAUSA

Africa CDC ta jaddada muhimmancin kara yawan gwajin cutar COVID-19 da binciko masu cutar

2021-01-29 13:06:25 CRI

Hukumar dakile cutuka masu yaduwar ta Afrika CDC ta sake jaddada muhimmancin kara yawan gwajin cutar COVID-19 da kuma binciko masu dauke da cutar da nufin shawo kan cutar da kuma takaita bazuwarta a fadin nahiyar.

John Nkengasong, daraktan hukumar ta Africa CDC, yace yin gwaji ita ce hanyar farko ta yaki da annobar, saboda idan ba a gudanar da gwajin ba, to ana yakar cutar ne ba tare da sanin alkibla ba.

Yace akwai kuma bukatar gano mutanen da suke dauke da cutar, da killace su, da kuma yi musu magani, ya kara da cewa, ta hanyar taimakawa kasashen mambobin kungiyar tarayyar Afrika AU wajen kara gudanar da gwajin da gano mutanen dake dauke da cutar da killace su da yi musu jinya, za a iya samun nasarar shawo kan cutar da kuma takaita bazuwarta.

Yayin da adadin mutanen da suka kamu da cutar a Afrika ya kusa kaiwa miliyan 3.5, Africa CDC ta jaddada cewa, adadin masu kamuwa da cutar a kullum yana kara hauhawa a zagaye na biyu wanda ya zarce adadin zagayen farko.

Alkaluman baya bayan nan da Afrika CDC ta fitar ya nuna cewa, yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a nahiyar Afrika ya kai 3,494,117, ya zuwa safiyar ranar Alhamis, kana yawan mutanen da cutar ta kashe ya kai 87,937.(Ahmad)