logo

HAUSA

WHO tace sabon nau’in COVID-19 zata iya mummunar illa na tsawon lokaci a Afrika

2021-01-29 12:18:53 CRI

Hukumar lafiya ta duniya ta ce, sabbin nau’o’in cutar COVID-19 da suka bulla za su iya haifar da mummunar illa ga kasashen Afrika da dama yayin da ake fargabar cutar zata iya shafe tsawon lokaci a zagaye na biyu a nahiyar, kuma za su iya kawo barazana ga fannin kiwon lafiyar nahiyar wanda tuni yake fuskantar matsaloli sanadiyyar barkewar cutar.

Matshidiso Moeti, daraktan hukumar WHO shiyyar Afrika, ya yi gargadi game da yaduwar sabbin nau’o’in cutar ta COVID-19 wadanda ake ganin suna da matukar hadari kuma za su iya kawo koma baya ga kokarin da ake na dakile bazuwar cutar a nahiyar.

Moeti ya bayyana cikin wata sanawar a Nairobi cewa, nau’in cutar wacce aka fara gano ta a kasar Afrika ta kudu tana yaduwa cikin sauri har ma ta fara bazuwa a wasu kasashen da ba na Afrika ba, kuma al’amarin akwai damuwa matuka kasancewar akwai yiwuwar cutar ta riga ta karade wasu daga cikin kasashe masu yawa na Afrika.

A cewar hukumar ta WHO, nau’in cutar mai suna 501 Y.V2, wacce aka fara ganowa a Afrika ta kudu ita ce ta yi sanadiyyar mummunar bazuwar cutar fiye da yadda aka yi tsammani a kasar ta biyu mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Nau’in cutar ta COVID-19 mai saurin bazuwa tuni an riga an gano ta a kasashen Botswana, Ghana, Kenya, da Zambia.

Baya ga haka, an kuma gano wani sabon nau’in cutar wacce asalinta daga Birtaniya a Gambia da Najeriya, yayin da ake cigaba da gudanar da bincike domin gano illar da cutar ke yiwa mutanen da suka kamu.(Ahmad)