logo

HAUSA

Jiangxi: An Taimakawa Mutane Wajen Saukaka Begen Gida Da Suke Yi Ta Kafar Bidiyo Kai Tsaye

2021-01-27 14:16:03 CRI

A kauyen Huikeng a garin Xinwan na gundumar Xiushui a yankin Jiujiang dake lardin Jiangxi na kasar Sin, yanzu haka mazauna wurin suna share fagen bikin bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ta wata hanyar da ba su taba bi ba a baya.

A kauyen Huikeng, kamar yadda su kan yi a baya wajen share fagen bikin bazara, mazauna wurin sun manna takardu masu dauke da kalmomin nuna fatan alheri a gefunan kofa, sun turara abincin Shaozi, sun kuma sarrafa awara. Amma a bana akwai wasu sauye-sauye. Suna share fagen wannan muhimmin bikin Sinawa ne ta hanyar kafar bidiyo kai tsaye, a kokarin taimaka wa ’yan kauyensu wadanda za su yi bikin bazara a wurin da suke aiki, a maimakon komawa gari, su saukaka begen gida da suke yi. Sa’an nan kuma mazauna kauyen sun sayar da amfanin gona ta kafar bidiyo kai tsaye zuwa sassa daban daban na kasar Sin, a kokarin wadatar da kansu.

“Ga abincin Shaozi da muke ci a kowane bikin bazara! Yana da dandano sosai. Ku duba, akwai abubuwa masu dadi da yawa a cikinsa.”

An gabatar da shahararren abincin Shaozi na gundumar Xiushui ta kafar bidiyo kai tsaye yayin da ake dafa shi. Abincin Shaozi na gundumar Xiushui, wani nau'in abinci ne da aka nika dankali mai zaki, sa'an nan a sanya abubuwa masu zaki, ko alewa, ko nama ko kayan lambu a cikin sa sai kuma a turara a kan wuta. Abincin garin wani, wata alama ce ta bikin bazara. Mazauna gundumar Xiushui suna cin abincin Shaozi a ko wane jajibirin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin. Fara dafa abincin na Shaozi, wata alama ce ta kaddamar da aikin share fagen bikin bazara a wurin. Luo Xinling, wata mazauna kauyen Huikeng ta ce, “Abincin Shaozi mai da’ira yana alamta cikakken iyali. Muna dafa abincin ne a ko wane bikin bazara da zummar kara jin dadin zaman rayuwa a sabuwar shekara.”

A bana, ’yan kauyen Huikeng da yawa sun amsa kiran gwamnati, za su yi bikin bazara a inda suke aiki a maimakon komawa gida. Liu Quanbao, wanda ke kula da harkokin sayar da amfanin gona ta kafar bidiyo kai tsaye, ya watsa shirin bidiyo kai tsaye kan yadda iyalinsa suke share fagen bikin bazara, ta yadda ’yan kauyensa da ba su koma gida a bana ba, suka samu damar saukaka begen gida da suke yi. Liu Quanbao ya ce, “A baya na shafe shekaru fiye da 10 ina aiki a wasu wurare. Na fahimci cewa, ana kara begen gida a bukukuwa. Ba mu hadu da mahaifa da ’ya’yanmu ba. Muna begensu. Don haka na fito da wannan dabara mai ma'ana. Za su yi bikin bazara tare da mu ta kafar bidiyo kai tsaye.”

Bayan Liu Quanbao ya watsa shirin bidiyo kai tsaye kan yadda ake dafa abincin Shaozi, ya je gidan Fang Xinguo, inda yake amfani da wani babban dutse wajen nika wake domin samun awara. Liu Quanbao ya ci gaba da watsa shirin bidiyo kai tsaye.

Da ganin yadda ake dafa abinci iri daban daban domin share fagen bikin bazara, ’yan kauyen Huikeng da za su yi bikin bazara a inda suke aiki, sun bayyana begen gida da suke yi cikin shirin bidiyon.

Liu Quanbao ya bayyana mana cewa, “Ko da yake akwai nisan kilomita dubu dubai a tsakaninmu, amma kallon yadda ake share fagen bikin bazara ta kafar bidiyo kai tsaye ya rage nisan da ke tsakaninmu. Muna share fagen bikin bazara tara kamar yadda muka saba bi a baya.”

A baya mazauna Huikeng su kan sayar da yawancin amfanin gona a wurare makwabta da kansu. Liu Quanbao ya kware ne wajen sayar da kaya a kan Intanet, don haka ya hada kai da ’yan kauyensa da dama, suka taimaka wa mazauna kauyen sayar da amfanin gona ta kafar bidiyo kai tsaye zuwa sassa daban daban na kasar Sin baki daya, har ila yau ’yan kauyensa daya sun samu damar kara sanin yadda ake share fagen bikin bazara a kauyensu, duk da ba su koma gida ba. Fasahar zamani ta rage nisan da ke tsakanin mutanen da ke aiki a wurare masu nisa da kuma iyalansu da ke gida. Liu Quanbao ya yi fatan cewa, karin mutane za su kara saninsu kan zaman rayuwar ’yan kauyensa mai dadi ta kafar bidiyo kai tsaye. Liu ya ce, “A shekarun baya, an fara amfani da Intenat a kauyenmu, inda kuma ake kai kaya a wurin, ana kara raya kauyenmu da kyau. Muna fatan ’yan kauyenmu wadanda suke aiki a sassa daban daban a kasarmu za su kara sanin ci gaban kauyenmu. An rage nisan da ke tsakaninmu da mutanen da ke sauran wurare. Muna fatan karin mutane za su zo kauyenmu ziyara.” (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan