logo

HAUSA

Yawan mutanen da suka kalli shirye-shiryen bikin bazara na bana ya wuce biliyan 1 da miliyan 232

2020-01-26 16:16:43 cri

Yawan mutanen da suka kalli shirye-shiryen bikin bazara na bana ya wuce biliyan 1 da miliyan 232

An cimma nasarar watsa shirye-shiryen bikin kade-kade da raye-raye na murnar shiga sabuwar shekara ta gargajiya ta kasar Sin na bana wanda babban gidan rediyo da talabijin na kasar wato CMG ya tsara, wanda ya karya bajinta na watsa shirye-shirye ta hanyar amfani da kafofin watsa labaru iri daban daban.

Yawan mutanen da suka kalli shirye-shiryen bikin bazara na bana ya wuce biliyan 1 da miliyan 232

Bisa kididdigar da aka yi, an ce gidajen talibijin 225 na kasar Sin sun watsa shirye-shiryen bikin kai tsaye, kafofin watsa labaru kusan 600 na kasashe da yankuna sama da 170 sun watsa labarai game da bikin na bazara. A yayin da ake watsa shirye-shiryen, wadanda suke kallon bikin ta hanyoyin talabijin, yanar gizo, dandalin sada zumunci da dai sauransu ya kai biliyan 1.232, ciki har da mutane miliyan 606 wadanda suka kalli shirye-shiryen kai-tsaye har sau biliyan 1.116 ta kafofin watsa labarai na zamani.(Bilkisu)