logo

HAUSA

Ana sa ran fasinjoji biliyan 1.7 za su yi bulaguro a lokacin bikin bazarar Sin

2021-01-21 09:36:16 CRI

A jiya Laraba ma’aikatar sufurin kasar Sin ta bayyana cewa, ana sa ran kimanin fasinjoji kusan biliyan 1 da miliyan 700 ne za su yi tafiye tafiye a lokacin bikin bazarar kasar dake tafe.

Ana tsammanin fasinjojin kusan miliyan 40 ne za su yi tafiye-tafiye a kullum a tsawon kwanaki arba’in da za a shafa ana tafiye-tafiyen, inda adadin zai karu da sama da kashi 10 bisa 100 idan an kwatanta da na shekarar 2020, Wang Xiuchun, jami’in ma’aikatar sufurin ya bayyanawa taron manema labarai.

Sai dai adadin ya ragu da kashi 40 bisa 100 idan an kwatanta da na shekarar 2019, in ji Wang.

Bulaguron bikin bazarar, wanda aka fi sani da chunyun, za a shafe tsawon kwanaki 40 wato daga ranar 28 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Maris na wannan shekarar.(Ahmad)