logo

HAUSA

Yawan masu kallon shirye-shiryen bikin bazara na bana ya karu sosai bisa na shekarun baya

2020-01-25 16:18:22 cri

Yawan masu kallon shirye-shiryen bikin bazara na bana ya karu sosai bisa na shekarun baya

Da karfe 8 na daren jiya Juma'a, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG a takaice, ya gabatar da bikin kade-kade da raye-raye domin taya al'ummar kasar murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar.

Bikin dai na kunshi da shirye-shirye masu kayatarwa da dama, ciki har da kade-kade da raye-raye, da wasan kwaikwayo, da wasan tattaunawa cikin raha, da wasan Kongfu, da wasan dabo, da kundunbala da dai sauransu. A waje guda kuma, bikin na bana ya dora muhimmanci kan wasu muhimman batutuwa da ke jawo hankalin al'umma, ciki har da wani shiri da ya bayyana yadda masu aikin jinya, da jama'a ke yaki da cutar numfashi da ta bulla, don bayyana niyyar Sinawa ta tunkarar cutar.

Yawan masu kallon shirye-shiryen bikin bazara na bana ya karu sosai bisa na shekarun baya

Rahotanni sun nuna cewa yawan masu kallon bikin na bana ya karu sosai bisa na baya. Bisa kididdigar da aka yi, an ce ya zuwa karfe 12 na daren ranar 24, yawan wadanda suka kalli shirye-shiryen da aka watsa kai tsaye, ta kafofin sadarwa na zamani ya kai biliyan 1,116, adadin ya kuma kai miliyan 589 ta kafar talibijin. Ban da wannan kuma, akwai kafofin watsa labaru na kasashen ketare sama da 560 da suka watsa shirye-shiryen bikin ko labarin bikin. Kana wadanda suka kalli bikin ta hanyoyin dandalin sada zumunci na Youtube da Facebook kuwa, sun wuce miliyan 24.62. (Bilkisu)