logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi farar dabara game da shirinta na fara riga-kafin COVID-19

2020-12-21 15:19:11 CRI

Kasar Sin ta yi farar dabara game da shirinta na fara riga-kafin COVID-19

Masu hikimar magana na cewa, “Abin da babba ya hanyo, yaro ko ya hau kan tsauni ba shi hangowa”. Tun bayan da aka samu rahotannin barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a farkon wannan shekarar, mahukunta kasar Sin sun tsaya kai da kafa ba-dare-ba-rana, domin ganin an samu zarafin dakile kaifin annobar. Koda yake, kasar ta yi hobbasa matukan wajen dakile annobar abin da masu salon magana ke cewa, “a jefi tsuntsu biyu da hoge daya”. Wato a lokacin da kasar ke kokarin dakile cutar COVID-19 a cikin gidan kasar, a hannu guda kuma tana kokarin tallafawa sauran kasashen duniya wajen dakile bazuwar cutar. Batun samar da alluran riga-kafi shi ne babban makamin da masana cutuka masu yaduwa na kasa da kasa suka bayar da shawarar a gaggauta samarwa domin kashe kaifin annobar da kuma dakile ta daga doron duniya. Yayin da kasashen duniyar suka dukufa wajen nazarin samar da alluran riga-kafin cutar ta COVID-19, mahukunta kasar Sin sun yi kyakkyawa nazari da hangen nesa game da matakan da suka dace a bi yayin fara amfani da riga-kadin cutar a kasar. Kamar yadda hukumar lafiya ta kasar Sin ta sanar, za a fara yi wa wasu muhimman rukunonin jama’a allurar riga-kafin COVID-19 a lokacin hunturu da bazara. Yayin wani taron manema labarai a karshen wannan mako, jami’in hukumar takaita yaduwar cututtuka na kasar Sin, Cui Gang, ya ce za a yi amfani da wani shirin bayar da riga kafi mai matakai 2, a mataki na farko, za a fara ba da riga kafin ga wasu rukunonin da suka hada da wandanda ke lura da kayayyakin da ake shigo da su kasar, da ma’aikatan wuraren bincike a tashoshin ruwa, da na bangaren kebe wadanda suka kamu, da bangaren sufurin jiragen sama, da na motocin haya, da kasuwannin kayan gwari, da ma’aikatan lafiya, da kuma jami’ai masu aikin takaita yaduwar cututtuka. Cui Gang, ya ce shirin bayar da riga kafin zai kuma shafi wadanda ke shirin zuwa aiki ko karatu a kasashe da yankunan da suka fi fuskantar barazanar yaduwar cutar da kuma wadanda ke kan matsakaicin matakin barazanar harbuwa da cutar. A cewarsa, wannan zai taimaka wajen ragewa kasar matsi ta fuskar kandagarki da takaita shigo da cutar, da kuma rage hadarin barkewarta a kasar. Ya kara da cewa, mataki na 2 shi ne, bisa la’akari da amincewa da allurar shiga kasuwa, kasar Sin za ta fara amfani da ita, inda za ta rika ba mutane da dama. Wannan matakin zai dakile yaduwar cutar a cikin kasar. Kawo yanzu dai, riga-kafin kasar Sin ya shiga matakin gwaji na karshe, inda ake gwajin nau’o’i 5 kan mutane. Ko shakka babu, wadannan matakai da mahukuntan kasar suka dauka na tsara shirin bayar da riga kafin mataki-mataki zai taimaka wajen cimma nasarar dakile annobar a kasar baki daya. (Ahmad Fagam)