logo

HAUSA

Labarin kawar da talauci na kauyen Longtian bisa hadin gwiwa tsakanin yankunan gabashi da yammacin kasar Sin

2020-12-21 14:42:02 CRI

Labarin kawar da talauci na kauyen Longtian bisa hadin gwiwa tsakanin yankunan gabashi da yammacin kasar Sin

A karshen shekarar 2020, kasar Sin ta kammala aikin kawar da talauci a sabon zamani kamar yadda aka tsara. Bayan shekaru 8 na yaki da talauci, kasar Sin ta warware matsalar da talauci da wasu mutane ke fuskanta, wadanda kudin shigarsu ba sa iya biyan bukatun zaman rayuwarsu, da kawar da talauci da yankuna ke fuskanta baki daya, kuma kusan matalauta miliyan 100 sun fita daga kangin talauci.

Ta yaya aka cimma wannan buri? Za mu iya hangowa daga labarin rage talauci da samun wadata a kauyen Longtian dake gundumar Wanshan ta birnin Tongren na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin, daga bakin wakiliyarmu Bilkisu.

Kafin shekara ta 2017, kauyen Longtian, wanda ke karkashin gundumar Wanshan, ya kasance wuri mai nisa da aka sani da yankin karkara mara kyau, wanda kuma aka mayar da shi a matsayin kauyen dake fama da talauci mai tsanani a yankunan tsaunuka. Hanyar tabo a cikin kauyen ita ce hanya daya kadai dake hade shi da duniyar waje. A cewar mazaunan kauyen, halin da suke ciki a lokacin kama da " Duk an lullube su cikin kasa a lokacin rani, kuma an rufe su da laka a lokacin damina." Babu ruwan sha a kauyen, a yawancin lokaci, mazauna kauyen sun yi amfani da ruwa bisa dogaro da gwamnati. Ban da wannan kuma, babu masana'antu a kauyen, mazauna su kan fita ci rani, ko yin noma a gida don ciyar da iyalansu, matsakaicin yawan kudin shigar da kowanensu ya samu a kowace shekara bai wuce RMB yuan 4,000 ba. A cikin gidaje 294 da ke kauyen, 52 na fama da talauci. Yadda za a kawar da talauci da samun wadata ya zama matsala mafi gaggawa da kauyen Longtian ke fuskanta.

A matsayinsa na abin misali wajen hadin gwiwa don kawar da talauci tsakanin sassan gabashi da yammacin kasar, tun daga shekarar 2016, yankin raya kimiyya da fasaha na zamani na birnin Suzhou na lardin Jiangsu dake gabashin kasar ta Sin ta fara ba da taimako ga gundumar Wanshan. Yang Liang, mai kula da aikin rage talauci da yankin ya tura zuwa Wanshan, don taimakawa a kauyen Longtian, har yanzu yana iya tuna yadda kauyen yake a lokacin da ya isa wurin a karon farko.

“Daga idanun mutanen da ke kauyen, na ga amincewa da kuma fatan da suka nunawa ma'aikatan yaki da talauci. A lokacin, na yanke shawarar cewa, dole ne in yi kokarin jagorantar mazauna yankin fita daga kan tsaunuka da kuma kawar da talauci.”

Labarin kawar da talauci na kauyen Longtian bisa hadin gwiwa tsakanin yankunan gabashi da yammacin kasar Sin

Bisa ainihin halin da ake ciki da yanayin kasa da kauyen Longtian ke ciki, reshen jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na kauyen ya tsara wata babbar manufa, wato raya masana'antar kayan lambu don fitar da talakawan wurin daga talauci da kuma taimaka musu wajen samun wadata, kuma sun jagoranci kafa kungiyar hadin kai ta musamman ta manoma ta Longtian. Daga baya kuma, bisa taimako daga yankin raya kimiyya da fasaha na zamani na Suzhou, an samu kudin tallafi RMB kusan yuan miliyan 1 na fara aikin kungiyar hadin kan, kana kuma yankin raya kimiyya da fasaha ya dauki nauyin sayar da dukkan amfanin gona da kungiyar hadin gwiwar ta samar. Dogaro da tsarin kawar da talauci ta hanyar hadin kai a tsakanin masana’antu da sashen hadin gwiwa da kuma matalauta, an sanya hannu kan kwangila tare da gidaje 87 masu fama da talauci dake kauyen, kuma an kafa sansanonin dasa kayan lambu na zamani wanda fadin muraba’in ya kai yanki fiye da kadada 20. Bisa jerin matakan da aka dauka, ba kawai an warware matsalar amfani da filayen da aka bari a kauyen ba, har ma ya samar da aikin yi ga mazauna kauyen fiye da 120. A cikin shekara ta farko da aka kafa kungiyar hadin gwiwar, yawan kudin shiga da kowane mutumin kauye ya samu a ko wane wata ya karu da yuan 2,600 da wani abu. Game da haka, mazaunin kauyen Yang Jingqiu ya bayyana cewa,

“Da ma na kan yi aiki a waje a duk tsawon shekara. Ba gazawa wajen kula da iyalina kadai na yi ba, har ma da rashin samun kudin shiga da yawa a duk shekara. Tun bayan da muka shiga kungiyar hadin gwiwar harkar noma a kauyen, duk iyalanmu muna aiki a kauyen, yanzu muna iya kula da gida sosai, kana muna samun kudi fiye da da.”

Bayan warware matsalar samun bunkasar tattalin arziki bisa matakin farko, sai aka fara la’akari da yadda za a inganta rayuwar al'adu ta mazauna kauyen. Yang Liang ya ce,

“Kawar da talauci shi ne matakin farko da muka dauka. Jami’ai masu rage talauci bai kamata su gamsu da taimakawa matalauta kawar da talauci kadai ba, abu mafi mahimmanci shi ne, yadda za a kara jagorantar su cimma burin tabbatar da zaman rayuwa bisa matsakaicin karfi, musamman ma biyan bukatunsu kan rayuwar al'adu.”

Kauyen Longtian ya jawo kudin yuan dubu 700 daga yankin raya kimiyya da fasaha na zamani na Suzhou, don kafa cibiyar ba da hidima ga mazauna, an kara dakin kiwon lafiya, dakin karatu, da kuma dakin ayyukan al'adu da dai sauransu.

Shekara daya kadai aka dauka don kawar da talauci a kauyen Longtian, labarin ya nuna yadda aka kawar da talauci a duk fadin kasar Sin. (Bilkisu)