logo

HAUSA

An fara amfani da rukunin layukan dogo masu saurin gudu mai lamba CR300 a kasar Sin

2020-12-21 14:01:34 CRI

Kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin ya ce, a kwanan nan  aka soma amfani da rukunin layukan dogo masu saurin gudu mai lamba CR300, wanda saurinsa ya kai kilomita 250 a kowace awa. Kawo yanzu, ana amfani da dukkan layukan dogo masu saurin gudu da ake kira CR wadanda saurinsu ya kai kilomita 160 zuwa 350 a kowace awa, al’amarin da ya shaida cewa sana’ar kirkikre-kirkiren fasahohin layukan dogo ta kasar Sin ta samu babban ci gaba.

A yayin da kasar Sin take aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 13, kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na Sin ya hada kai tare da sauran wasu kamfanoni gami da cibiyoyin nazari da jami’o’i daban-daban, domin kirkire-kirkiren na’urorin zirga-zirgar jiragen kasa masu saurin gudu, kuma kwalliya ta riga ta biya kudin sabulu.(Murtala Zhang)