An bude filin jiragen sama na tsaunin Xiannu na birnin Chongqing
2020-12-21 13:57:59 CRI
Filin jiragen sama na tsaunin Xiannu na birnin Chongqing shi ne filin jiragen sama na al’umma na biyar da aka gina a birnin Chongqing na kasar Sin. An gina wannan filin jiragen sama a kan tsaunin da tsayinsa ya kai mita 1745.04, kuma, gaba daya fadin filin jiragen saman ya kai muraba’in mita dubu 6. (Maryam)