logo

HAUSA

Fasahar Kasar Sin Na Taimakawa Najeriya Wajen Inganta Zirga-Zirga Tare Da Bunkasa Al’Umma Da Kiyaye Muhalli

2020-12-20 16:20:43 CRI

 

Fasahar Kasar Sin Na Taimakawa Najeriya Wajen Inganta Zirga-Zirga Tare Da Bunkasa Al’Umma Da Kiyaye Muhalli

Kwanan baya, an fara gwajin layin dogo dake tsakanin Lagos da Ibadan dake amfani da jirgin kasa mai saurin tafiya, wanda ya kasance irinsa na farko a yammacin Afrika dake da hanyoyi biyu wato kaiwa da kawowa. Wannan layin dogo na da tsawon kilomita 156 dake hada birnin Lagos da Ibadan, za a kwashe awoyi biyu a zuwa ko kuma dawowa tsakanin wadannan birane biyu, matsayin saurin tafiyar ya kai kilomita 150 a sa’a guda.

Wannan layin dogo zai taimaka wajen kyautata halin zirga-zirga a yankin, ta yadda za a kara karfin sufurin kayayyaki da bunkasa birane dake kan wannan layi. An ce, aikin shimfida wannan layin ya samar da guraben aikin yi fiye da 4000, tare da samar da damammaki ga sha’anin kayayyakin gine-gine da sana’ar gine-gine da dai sauransu. Wasu jami’an wuri na ganin cewa, wannan layi zai ingiza bunkasuwar tattalin arzikin wurin.

Fasahar Kasar Sin Na Taimakawa Najeriya Wajen Inganta Zirga-Zirga Tare Da Bunkasa Al’Umma Da Kiyaye Muhalli

Kamfanonin kasar Sin ba aikin gina ababen more rayuwa kawai suke yi ba a Najeriya, har ma suna yin iyakar kokarin kiyaye muhalli. Wata fasinja dake shiga wannan jirgi Madam Omora ta ce, kamfanin kasar Sin ba ma kawai ya shimfida wannan layi da fasaha mai inganci ba ne, har ma ya maida hankali kan kiyaye muhallin wurin, ga itatuwa da ya dasa da wasu na’urorin kiyaye muhalli da ya kafa.

A matsayin wani sabon ci gaba na raya shawarwar “Ziri daya da hanya daya” tsakanin Sin da Najeriya, layin dogon ya zurfafa hadin kan kasashen biyu. Kamata ya yi Sin da Najeriya su yi amfani da wannan zarafi mai kyau wajen kara bunkasa dangantakar kasashen biyu da ma raya tattalin arzikinsu mai dorewa cikin hadin kai. (Amina Xu)