logo

HAUSA

Duk Yunkurin Haddasa Tunzuri Tsakanin Kasar Sin Da kasashen Afirka Ba Zai Samu Nasara Ba

2020-12-19 17:25:09 CRI

Duk Yunkurin Haddasa Tunzuri Tsakanin Kasar Sin Da kasashen Afirka Ba Zai Samu Nasara Ba

Kwanan baya, bankin kasar Sin ya amince da rokon gwamnatin Najeriya dangane da neman rancen kudi da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 2.5, wanda za a yi amfani da su wajen shimfida bututun iskar gas tsakanin Ajaokuta da Kaduna da Kano. Yayin da madam Zainab Ahmed, ministar kudi da tsara shirin kasar Najeriya ta yi rangadin aiki a Ajaokuta da ke jihar Kogi, ta nuna cewa, shirin nan zai kawo wa Najeriya karin kudin shiga, in an kwatanta kudin da aka zuba a yanzu, tare kuma da samar da dimbin guraben aikin yi. Ta kuma yi imanin za a kammala aikin a daidai lokacin da aka tsara.

A ko da yaushe aka ambato batun rancen kudi daga kasar Sin, to, wasu su kan nuna kin yarda. Amma kamar yadda kasar Sin ta shigar da dimbin jarin waje a farkon lokacin da ta fara bude kofa ga ketare da yin gyare-gyare a gida, yanzu kasashen Afirka, wadanda suke kokarin raya kansu, suna matukar bukatar jarin waje, ta hanyoyin zuba jari da neman rancen kudi da dai sauransu. Kasashen Afirka sun nemi samun rancen kudi ne domin zuba jari kan ababen more rayuwar jama’a, a maimakon yin sayayya. Nan gaba kudaden da suke zubawa yanzu za su kawo wa kasashen Afirka alheri a fannonin tattalin arziki da zaman al’ummar kasa.

Ban da haka kuma, kasar Sin ba babban mai bai wa kasashen Afirka rancen kudi ba ne. Alkaluman da jami’ar Johns Hopkins ta Amurka sun shaida cewa, kasar Sin ta bai wa kasashen Afirka rancen kudi na dalar Amurka biliyan 114.4 baki daya daga shekarar 2000 zuwa 2016, adadin da ya kai kaso 1.8 cikin 100 bisa jimilar basussukan da ake binsu.

Kullum kasar Sin tana hada kai da kasashen Afirka ba tare da wata rufa-rufa ko kuma wani sharadin siyasa ba, kuma ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Afirka ba. Haka lamarin yake wajen daidaita basusukan da kasar Sin take bin kasashen Afirka. Don haka ba za a dora wa kasar Sin laifin yi wa kasashen Afirka tarkon bashi ba. Wasu kasashe ne suka yi wa kasashen Afirka gyaran fuska ta hanyar bin su basusuka a baya, lamarin da kasashen Afirka suka yi wa suka sosai. Alkaluman asusun ba da lamunin duniya wato IMF sun nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2019, kasashen Afirka da yawansu ya kai kaso 40 cikin 100 sun yi fama da matsalar bashi, amma bankunan kasashen Turai da Amurka da masana’antunsu ne suke bin yawancinsu.

A daidai lokacin da kasashen Afirka suke dukufa wajen farfadowa daga annobar cutar COVID-19, kasar Sin ta kara mai da hankali kan batun bashin da take bin su. Ta amsa kiran kungiyar G20 dangane da tsawaita lokacin biyan bashi da take bin kasashen Afirka. A yayin taron koli na musamman dangane da yaki da annobar COVID-19 cikin hadin gwiwar Sin da Afirka, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sanar da wasu muhimman matakan rage yawan basusukan da Sin take bin Afirka da kuma tsawaita lokacin biyan bashin.

Ba wanda zai iya boye gaskiya. Duk yunkurin da ake yi na haddasa tunzuri tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ba zai samu nasara ba. (Tasallah Yuan)