logo

HAUSA

An cimma burin tsabtar ruwa a dukkan birane da garuruwan jihar Xinjiang

2020-12-03 13:40:46 CRI

Bisa labarin da ofishin kula da gine-gine da raya birane da kauyuka na jihar Xinjiang ya bayar, an ce, ya zuwa yanzu, an cimma burin tsabtar ruwa a dukkan birane da garuruwa a jihar, yawan kamfanonin tsabtace ruwa da aka gina ya kai 111, a cikinsu guda 92 sun kai ma’aunin A na fitar da ruwa mai tsabta, yawansu ya karu da guda 70 idan an kwatanta da na shekarar 2017 a jihar.

Ban da wannan kuma, an cimma burin tsabtar ruwa da sake yin amfani da ruwa da kashi 85 cikin dari a karshen 2020 da aka tsara bisa shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 13 kafin lokacin da aka tsara. (Zainab)