logo

HAUSA

Xi Ya Gabatar Da Matsayar Kasar Sin Game Da Shawo Kan Kalubalolin Duniya

2020-11-23 15:43:12 CRI

Xi Ya Gabatar Da Matsayar Kasar Sin Game Da Shawo Kan Kalubalolin Duniya

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarwari da matsayar kasar Sin game da yadda za a tinkari manyan kalubalolin duniya a yayin da ya halarci tarukan gamayyar kasa da kasa iri daban daban a makon da ya gabata. Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya sanar da hakan a ranar Lahadi.

Shugaba Xi ya halarci taron kolin shugabannin kasashe mambobin BRICS, da taron kawance raya tattalin arzikin Asiya da Pacific (APEC), da kuma taron mambobi kasashen G20 daga ranar 17 zuwa 22 ga wannan wata.

Muhimman tarukan kasa da kasar sun gudana ne a daidai lokacin da duniya ke fama da barkewar annoba mafi muni a tarihi, wacce ta haifar da mummunar karayar tattalin arzikin duniya da kalubaloli masu tarin yawa da suka jefa al’ummar kasashen duniya cikin matsanancin hali.

A cewar mista Wang Yi, shugaba Xi ya zayyana matsayin kasashen BRICS mai cike da tarihi, da kungiyar APEC, da G20 a daidai lokacin da duniya ke fuskantar sauye-sauye, inda ya gabatar da wasu muhimman shawarwari 23, game da bukatu da kuma matakan da ya dace a dauka domin tinkarar ayyukan yaki da annobar COVID-19 tare da kokarin inganta makomar tattalin arzikin duniya, da kyautata zaman rayuwar al’umma, ta hanyar hadin gwiwar kasa da kasa a bayan kawo karshen annobar, da yadda za a karfafa tsarin tafiyar da tattalin arzikin duniya.

Bayanai da dama da aka fitar na bayan kammala tarukan sun bayyana matsayar kasar Sin da aniyar kasar, kana sun bayyana tunani da hikimar kasar Sin, a cewar Wang.

Wang ya ce, kasashen duniya da dama sun yi tsokaci game da kalaman shugaba Xi a lokacin gudanar da tarukan game da bayanan da shugaban ya yi dangane da yadda mu’amalar kasa da kasa ya kamata ta kasance bayan kawo karshen annobar.

Game da batun hadin gwiwar yaki da annobar COVID-19, Wang ya ce, shugaba Xi Jinping ya gabatar da cikakkun bayanai masu cike da hikima dangane da tunanin kasar Sin da shawarwarinta game da yadda ya kamata duniya ta tinkari yaki da annobar COVID-19.

Daga cikin tunani da shawarwarin sun shafi batun mayar da rayukan jama’a da ci gabansu a gaban komai, da batun yin hadin gwiwa da nuna goyon bayan juna wajen yakar annobar COVID-19, da kuma batun nuna goyon baya kan rawar da hukumar lafiya ta duniya WHO ke takawa wajen yaki da annobar ta COVID-19, in ji Wang.

Wang ya ce, Xi ya kuma tabbatar da aniyar kasar Sin na cigaba da nuna goyon baya da shiga a dama da ita a hadin gwiwar kasa da kasa game da samar da alluran rigakafin cutar COVID-19, da tabbatar da nasarar shirin hadin gwiwar samar da rigakafi na COVAX wanda hukumar WHO ke goyon bayansa, Sin za ta rarraba rigakafinta ga sauran kasashen duniya, musamman kasashe masu tasowa, kana za ta ci gaba da yin aiki tukuru domin ganin alluran rigakafin sun amfanawa al’ummar duniya ta yadda za su iya samunsa cikin sauki ga mutanen duniya baki daya.

A cewar Wang Yi, shawarwarin da shugaba Xi ya gabatar sun kara kaimi ga hadin gwiwar kasa da kasa a yaki da annobar COVID-19, kuma sun karawa al’ummar duniya kwarin gwiwa wajen samun nasarar yakar annobar.

Game da batun farfadowar tattalin arziki kuwa, Wang ya ce, Xi ya gabatar da wasu jerin hanyoyin da za su kasance mafita wajen farfadowar tattalin arzikin duniya, ta hanyar rungumar tsarin bude kofa, da yin kirkire kirkire, kana da cikakken tsarin raya ci gaban duniya ta hanyar amfani da makamashi mai tsafta.

Wang ya ce, Xi ya kara gabatar da matsayar kasar Sin game da batun tafiyar da yanayin tattalin arzikin duniya a lokacin taron kolin G20, ya zayyana muhimmancin kiyaye ka’idoji, da mutunta dokoki, gami da rungumar tsarin tattalin arziki na zamani.

Jawabin Xi zai taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauye sauye ga tsarin tafiyar da tattalin arzikin duniya a halin da ake ciki yanzu da kuma a nan gaba, in ji Wang.

A taron kolin BRICS kuwa, jawabin Xi ya samar da kwarin gwiwa ga sabbin kasuwanni dake tasowa da kuma kasashe masu tasowa wajen yin hadin gwiwa domin tinkarar kalubaloli tare, da fadada hanyoyin ci gaba a gare su, da kuma yin kaimi wajen zaburar da kasashen duniya a daidai lokacin da duniyar ke fama da rashin tabbas.

A taron tattaunawar APEC, shugaba Xi da kasar Sin sun yi maraba da sanya hannu kan yarjejeniyar kawancen raya tattalin arzikin kasashen Asiya da Pacifi na RCEP, kana matakin zai samar da kyakkyawan sakamako na bunkasa cigaban yarjejeniyar shiyyar ta CPTPP.

Wannan muhimmiyar sanarwa ta kara jaddada matsayin kasar Sin bisa kudirinta na kara bude kofa da kuma yadda kasa da kasa suke kara lamince mata, a cewar mista Wang Yi.

Jawaban Xi sun bayyana matsayar Sin na kokarin tabbatar da hadin gwiwar bangarori daban daban don kawar da annobar COVID-19, da cin moriya tare, ta hanyar hadin gwiwar bangarori daban daban karkashin sabuwar dangantaka da huldar kasa da kasa domin samar da kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama. (Ahmad Fagam)