logo

HAUSA

Yadda Xi Jinping ke kallon Yankin Pudong

2020-11-12 20:47:11 CRI

Yadda Xi Jinping ke kallon Yankin Pudong

Yadda Xi Jinping ke kallon Yankin Pudong

Yankin Pudong dake birnin Shanghai na kasar Sin wani yanki ne da aka kebe domin raya masana’antu da cinikin kasa da kasa, cikin shekaru 30 da suka wuce. A yau Alhamis, an gudanar bikin murnar cika shekaru 30 da fara raya yankin Pudong, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi. 

Yadda Xi Jinping ke kallon Yankin Pudong

Yadda Xi Jinping ke kallon Yankin Pudong

Shugaban ya nuna yabo sosai kan nasarorin da aka samu a yankin, inda ya ce, yawan GDPn yankin ya haura daga Yuan biliyan 6 a shekarar 1990, zuwa Yuan biliyan 1270 a shekarar 2019. Yanzu haka yankin, da fadinsa ya kai kashi 1 bisa 8000 na fadin kasar, yana samar da GDPn da ya kai kashi 1 cikin kashi 80 na GDPn daukacin kasar, da kashi 1 cikin kashi 15 na yawan kayayyakin da ake shigo da fitar da su a kasar. Ban da wannan kuma, tsawon rayuwar jama’ar yankin ya karu daga shekaru 76 a shekarar 1993 zuwa shekaru 84 a yanzu. Kana fadin gidan zama da kowane mutum ke samu a yankin ya karu daga mita 15 a shekarar 1993 zuwa mita 42 a halin yanzu. (Bello Wang)

Bello