logo

HAUSA

Xi zai halarci taron kolin BRICS karo na 12 da taron APEC karo na 27 da kuma taron kolin G20 karo na 15

2020-11-12 11:58:15 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta sanar a yau cewa, bisa goron gayyatar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya aika masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron kolin kasashen BRICS karo na 12 a ranar 17 ga watan Nuwamba, sannan bisa goron gayyatar da firaministan kasar Malaysia Muhyiddin Yassin ya aika masa, shugaba Xi Jinping zai halarci taron kolin shugabanni kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Asiya da yankin tekun Fasifik ta fuskar tattalin arziki wato APEC karo na 27 a ranar 20 ga watan Nuwamba, kana a bisa goron gayyatar da sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na kaasar Saudi Arabia ya aika masa, shugaba Xi Jinping zai halarci taron kolin G20 karo na 15 a ranakun 21 zuwa 22 ga watan Nuwamba. Dukkan tarukan uku za a gudanar ne ta kafar bidiyo. Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci tarukan kana zai gabatar da muhimman jawabai daga birnin Beijing.

Sannan a yayin wani taron manema labaru daban  da aka shirya, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, yayin da annobar COVID-19 ke ci gaba da addabar wasu sassa na duniya, da ma yadda tattalin arzikin duniya ke kara shiga wani hali na karaya, tarukan koli guda uku, za su taka rawa wajen karfafa hadin gwiwa kan yaki da wannan annoba, da kara farfado da tattalin arzikin duniya, da inganta tsarin tafiyar da tattalin arzikin duniya, da bunkasa musayar tattalin arziki tsakanin shiyyoyi.

Ana kuma sa ran shugaba Xi zai gabatar da jawabai, inda zai yi karin haske kan matsayin kasar Sin tare da gabatar da shawarwari kan yin hadin gwiwa. (Ahmad, Ibrahim)

Ahmad Fagam