logo

HAUSA

Xi Jinping Ya Yi Rangadi A Lardin Jiangsu Don Tsara Ayyukan Dake Da Alaka Da Ruwa

2020-11-14 16:50:53 CRI

Xi Jinping Ya Yi Rangadi A Lardin Jiangsu Don Tsara Ayyukan Dake Da  Alaka Da Ruwa

Bayan ya halarci bikin murnar cika shekaru 30 da raya yankin Pudong na birnin Shanghai, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara rangadi a lardin Jiangsu dake dab da kogin Yangtze na kasar, inda ya mai da hankali kan yadda ake kula da koguna, da aikin janyo ruwa daga kogunan yankin kudu don samar wa arewacin kasar dake da karancin ruwa.

Da ma lardin Jiangsu ya kasance wani muhimmin bangare na shirin gina zirin tattalin arziki a dab da kogin Yangtze na kasar Sin. Bisa manufar da shugaba Xi ya tabbatar, ya kamata a raya tattalin arzikin lardin da ya zama kan gaba a kasar Sin, kana a himmantu wajen kare muhallin da hallitu.

Sa’an nan a jiya Juma’a, Xi Jinping ya yada zango a birnin Yangzhou dake tsakiyar lardin Jiangsu, wanda ya kasance a dab da koramar da aka haka, da ya hade biranen Beijing da Hangzhou. Inda ya ziyarci wata madatsar ruwa, da ta kasance wani bangare na babban aikin janye ruwa daga kogunan kudancin kasar Sin, da samar da shi ga arewacin kasar dake da karancin ruwa. Shugaban ya ce ya kamata a yi kokarin gudanar da aikin na jan ruwa da kyau, kana dole a yi tsimin ruwa, musamman ma a yankunan arewacin kasar.

Ana sa ran ganin rangadin da shugaban ya yi a lardin Jiangsu zai taimakawa manyan shugabannin kasar wajen tsara ayyukan raya tattalin arzikin kasar cikin shekaru 5 masu zuwa, musamman ma a fannonin kare muhalli, da samun ci gaba mai inganci. (Bello Wang)

Bello