logo

HAUSA

Kasar Sin na maraba da dukkan kasashe da yankuna da kamfanonin dake muradin hadin gwiwa da ita

2020-11-19 11:49:14 CRI

Da yake jawabi yayin taron shugabannin kamfanoni na kungiyar APEC, wato kungiyar hadin kan kasashen Asiya da tekun Pasific a yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta shiga a dama da ita wajen rabon nauye-nauye da shiga cikin tsarin samar da kayayyaki na duniya, da kuma fadada musaya da hadin gwiwa da sauran kasashe.

Ya kara da cewa, kasar Sin za ta yi maraba da dukkan kasashe da yankuna da kamfanonin dake sha’awar hada gwiwa da ita. Ya kuma jaddada cewa, akwai bukatar a ci gaba da inganta dunkulewar tattalin arzikin yankin, da gaggauta kirkire-kirkiren ci gaba, da hada yankuna da cimma dawwamammen ci gaba na bai daya, da kokarin cimma burika daki-daki tare da samar da moriya ga al’ummun yankin Asiya da Fasifik.

A cewarsa, zurfafa hadin gwiwa ta fuskar ci gaba da tattalin arzikin yankin Asiiya da Fasifik zai ci gaba da bayyana karin kuzari. (Fa’iza Mustapha)