A jiya ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bugawa takwaransa na kasar Canada Mista Justin Trudeau wayar tarho, inda ya taya shi murnar lashe zaben kujerar sabon firaministan kasar. A cewarsa Sin na fatan kara mu'ammala tsakanin shugabannin kasashen biyu, da kara amincewa da juna ta fuskar siyasa, da habaka hadin gwiwa ta fuskar ciniki, ba da ilmi da al'adu da harkokin matasa da sauransu, har kuma da kiyaye zaman lafiyar shiyya-shiyya da na duniya da samun lafiya da kwanciyar hankali da bunkasuwar duniya baki daya.
A nasa bangare, Mista Justin Trudeau ya ce, kasashen biyu na da makoma mai kyau ta fuskar hadin kai, kara inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta dace ga moriyarsu da ma ta duniya baki daya. Sabuwar gwamnatin kasar Canada na dora muhimmanci matuka kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kuma tana fatan shugabanninsu za su kara mu'ammla a tsakaninsu, da hara hadin gwiwa a fannoni daban-daban, ta yadda za a daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa sabon matsayi, da bude sabon shafi dangane da hadin gwiwa a tsakaninsu a fannoni daban-daban. (Amina)