Mr Li ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da tsohon sakataren baitul malin Amurka Henry Paulson, inda ya toba matsalar da ake fuskanta a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya a wannan shekara da kwangaba-kwangaban da ba a saba gani ba a kasuwannin hannayen jarin kasar.
Firaminista Li ya ce, matakan da kasar Sin ta dauka sun yi daidai da tsarin kasa da kasa da kuma yanayin da kasar Sin ke ciki. Kuma kasar Sin ta inganta yadda ta auna darajar kudin kasar na RMB ta yadda zai dace da ci gaban kasuwannin hada-hadar kudi ta duniya.
Ya kuma bayyana cewa, ci gaban kasar Sin ya dogara ne ga shirin gyare-gyare a cikin gida da kuma bude kofa ga kasashen wajen, don haka kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da wadannan matakai.
Bugu da kari, Mr Li ya ce, kasar Sin za ta fadada yin gyare-gyare a yankin ciniki cikin 'yanci na birnin Shanghai sannan ta kara darajar musayar kudin kasar sannu a hankali.
A nasa bangaren Henry Paulson ya bayyana farin ciki dangane da yadda masana'antun kasar Sin ke kara gogayya sakamakon shirin nan na bude kofa.(Ibrahim)