in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya ce za a kara kuzarin kamfanonin gwamnati ta hanyar gyaran fuska
2015-09-21 11:58:13 cri

A ranar 18 ga wata, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya kira taron tattaunawa kan batutuwan da suka shafi yi wa kamfanonin dake karkashin ikon mallakar gwamnatin kasar gyaran fuska da yadda za a bunkasa su yadda ya kamata, taron ya samu halartar shugabannin manyan kamfanonin gwamnatin kasar Sin da dama.

Yayin taron, Keqiang ya ce, kamfanonin gwamnati suna da muhimmanci sosai ga bunkasar kasar Sin, kuma za'a iaya cewa suna taka muhimmiyar rawa a fannin tattalin arziki da siyasa, musamman wajen kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar, da sake habaka ci gaban kasar ta Sin. To sai dai a halin da ake ciki, suna fuskantar matsaloli, misali tsarin da ake gudanarwa ba shi da inganci sosai ba, shi ya sa ake ganin lokaci ya yi da za'a yiwa kamfanonin garambawul.

Li Keqiang ya ce, ya kamata a kara mai da hankali kan aiwatar da ayyukan da za su kawo albarkar kasa, da aikin kirkire-kirkire, ta yadda za a kara habaka karfin gogayya na kamfanonin.

Hakazalika, Li Keqiang ya kara da cewa, idan ana son kara zurfafa gyaran fuskar da ake yi wa kamfanonin gwamnati a Sin, ya kamata a kara bude kofa ga kasashen waje.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China