Mr. Li ya bayyana hakan ne lokacin da yake shugabantar taron kara wa juna sani kan halin da ake ciki ta fuskar tattalin arziki, taron da ya samu halartar gwamnonin wasu lardunan kasar Sin.
A yayin taron, mahalartan suna ganin cewa, a shekarar da ake ciki, halin da tattalin arziki kasar Sin ke ciki a gida da waje yana da sarkakiya matuka, kuma ana fuskantar kalubaloli iri iri. Gwamnatin tsakiya ta dauki kwararan matakan daidaita manufofin bunkasa tattalin arziki, kuma ta kara zurfafa yin gyare-gyare a cikin gida ta yadda kwaliya za ta biya kudin sabulu dangane da tabbatar da samun dawaumammen ci gaban tattalin arzikin kasar.
Bugu da kari, Li Keqiang ya jaddada cewa, yanzu kasar Sin tana kokarin sauya salon bunkasa tattalin arzikinta, don haka ya kamata bangarori daban daban su yi kokarin warware duk wasu matsalolin da za su iya kunno kai cikin hadin gwiwa domin tabbatar da cimma burin neman bunkasa da aka sanya gaba a wannan shekara. (Sanusi Chen)