Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bukaci da a yi garambawul ga harkokin kudaden kasar, da kuma bullo da sabbin dabaru domin bunkasa tattalin arkin kasar Sin.
A wata sanarwa da mista Li ya fitar a jiya Lahadi, bayan kammala wani taron musayar ra'ayoyi don duba halin da tattalin arziki da masana'antun kasar Sin ke ciki a ranar Juma'ar da ta gabata, ya bukaci bankuna da sauran ma'aikatun kudin kasar da su bullo da sabbin dabarun zamani, ta yadda tattalin arizikin kasar zai samu kyakkyawan yanayin domin samun ingantacciyar makoma.
Li, ya tattauna da wakilai daga bankuna da suka hada da bankin raya aikin gonar kasar Sin da bankin gina kasar Sin da bankin ajiye kudi na gidan wayar kasar Sin da da kuma kamfanin inshurar jama'ar kasar Sin.
Ya ce, dole ne bankunan kasar su dauki kwararan matakai da suka shafi gudanar da hada hadar kudade, musamman wajen ba da rance da rage kudaden da suke caza daga abokan huldarsu, da inganta aikin tallafawa kananan sana'o'i.
Li, ya bukaci bankunan kasar da su kara bude kofa ga kasashen waje, musamman ma a yankunan ciniki maras shinge.(Ahmad Fagam)