A yayin ganawar, Mr. Li Keqiang ya ce, yana fatan bangarorin biyu za su hanzarta tattaunawar kafa asusun zuba jari na kasashen Sin da Turai, sabo da wannan ba ma kawai zai taimaka wajen kara zuba jari da yin hadin gwiwar hada-hadar kudi da bude kasuwa ta daban ga bangarorin biyu ba, har ma zai iya nuna wa sauran kasashen duniya cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan matsayin nuna goyon baya ga kokarin tabbatar da darajar kudin Euro da dunkulewar kasashe mambobin kungiyar EU.
Bugu da kari, Mr. Li Keqiang ya jaddada cewa, yanayin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki a bana yana gudana kamar yadda ya kamata, domin ba a sauya yanayin ci gaban da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki cikin dogon lokaci ba.
A nasa bangaren, Mr. Katainen ya bayyana cewa, bangaren EU yana son kara yin hadin gwiwa da kasar Sin kan manufofin bunkasa tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare, kuma ya amince tare da taimakawa kasar Sin wajen aiwatar da ajandar da ta tsara aiwatarwa game da manufofin yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofar ga kasashen waje. (Sanusi Chen)