A gun taron, an tsaida kuduri cewa, ya kamata a kara inganta gudanar da cinikayya ta hanyar amfani da yanar gizo a kauyuka, da kyautata yanayin raya irin cinikayya a kauyuka, da samar da yanayi mai kyau na kashe kudi, da yaki da sayar da kayayyaki masu yabu a kan internet, da kuma kara gabatar da manufofi masu dacewa don raya sha'anin.
Hakazalika kuma, an tsaida kudurin kara zuba jari, da jagoranci kananan hukumomi wajen kyautata manufofi da kara samar da kudin goyon baya da dai sauransu don cimma burin shimfida tsarin yanar gizo a kashi 98% na kauyukan kasar Sin a shekarar 2020. (Zainab)