in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da baki ma'aikata da suka samu lambar yabon sada zumunta
2015-09-30 20:58:30 cri

A yau da yamma ne, Mr. Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya gana da baki wadanda suke aiki a nan kasar Sin kuma suka samu lambar yabon sada zumunta ta shekarar 2015 da iyalansu a nan Beijing.

Mr. Li Keqiang ya bayyana cewa, "lambar yabon sada zumunta" ba ma kawai tana bayyana zumuncin dake tsakanin Sinawa da sauran 'yan kasashen duniya ba, har ma tana nuna muhimmcin tabbatar da zaman lafiya da neman samun ci gaban a duniya baki daya.

Kasar Sin tana son hada kai da sauran kasashen duniya wajen gina duniya mai kwanciyar hankali ta hanyar sada zumunta cikin sahihanci.

Sannan Li Keqiang ya nuna cewa, yanzu kasar Sin na kokarin neman ci gaba ta hanyar kirkiro sabbin fasahohin zamani da sabbin hanyoyin samun ci gaban tattalin arziki, tana kuma karfafa wa al'umma gwiwa da su raya sana'o'i da kansu, kuma su yi kokarin kirkiro sabbin fasahohin zamani, ta yadda za a iya sauya tsohon salon bunkasa tattalin arziki da a baya ya dogara da makamashin halittu da dimbin kwadago kawai, domin kokarin kyautata tsarin tattalin arziki da samun dawaumammen ci gaba mai inganci.

Mr. Li ya ce, kasar Sin tana maraba da kwararrun kasashen waje da su kirkiro sabbin fasahohin zamani da suke da sha'awa, kuma su raya sana'o'insu domin kokarin samun ci gaba a nan kasar Sin.

Bugu da kari, Li Keqiang yana fatan kwararrun kasashen waje dake nan kasar Sin za su ci gaba da ba da nasu shawarwarin da za su taimaka a kokarin da mahukunta ke yi na bunkasa kasar Sin. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China