02-Jan-2026
31-Dec-2025
31-Dec-2025
30-Dec-2025
27-Dec-2025
25-Dec-2025
24-Dec-2025
24-Dec-2025
A cikin shirinmu na yau, za a ba da labarin masana kimiyya da fasaha guda uku daga kasashen Afirka, wadanda suka bar kasashensu zuwa kasar Sin don lalubo bakin zaren daidaita matsalar rashin isasshen abinci da kasashensu ke fuskanta.
02-Jan-2026
Da yake shekarar 2025 ta riga ta tattara nata-i-nata tana mana bankwana, shirin namu zai yi waiwaye wanda masu karin magana kan ce adon tafiya game da alakar kasar Sin da Nijeriya a shekarar, wacce za mu iya cewa ta kasance mai matukar alfanu a fannin sake fasalta ci gaban cinikayya, da fasahar zamani, da kayayyakin more rayuwa musamman a kasar ta Nijeriya wacce ake wa lakabi da “Giwar Afirka". Idan ba a manta ba, daga farkon watan Janairun shekarar ta 2025, lokacin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, wanda har ila yau mamba ne a kwamitin koli na hukumar siyasa ta kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya ziyarci Abuja bisa al’adar da ministocin harkokin wajen Sin suka kiyaye tsawon shekaru, na fara kai ziyara yankin Afirka, an diga sabon dan ba na ciyar da alakar kasashen biyu gaba.
31-Dec-2025
29-Dec-2025
Shirin Duniyarmu A Yau na wannan karon, ya duba muhimman dabarun da kasar Sin ta sa gaba da yadda take kara kalailaice su domin tsara matakan ci gaban tattalin arzikinta da zamantakewa a cikin shekaru 5 masu zuwa. A farkon makon nan, firaministan kasar Li Qiang ya jaddada muhimmancin kara tace daftarin shirin bunkasa ci gaban kasa da kyautata zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15, wanda zai jagoranci manyan al'amurra da manufofin kasar a shekaru biyar masu zuwa. Wannan shirin na da nufin karfafa samar da ci gaba mai inganci, da karfafa kirkire-kirkire, da inganta tsarin tattalin arziki baki daya, da tabbatar da ci gaba mai dorewa da kyautata jin dadin jama'a.
24-Dec-2025