31-Aug-2025
30-Aug-2025
29-Aug-2025
29-Aug-2025
29-Aug-2025
28-Aug-2025
28-Aug-2025
27-Aug-2025
Damina a Habasha, wadda ke farawa daga watan Yuni zuwa Satumba a kowace shekara, na kara wa rayuwar tsirrai inganci. Gwamnati da mazauna wurin suna aiki tukuru don farfadowa gami da kiyaye muhallin halittu, inda sannu a hankali suke kan hanyar samun ci gaba mai kiyaye muhalli, kuma dabarun kasar Sin suna kara wa wannan ci gaban sauri. A cikin shirinmu na yau, zan ba ku labarin yadda kasar Sin ke taimaka wa Habasha ta fuskar dashen itatuwa, tare da hada kai da kasashen Afirka wajen bunkasa ci gaba mai kiyaye muhalli.
27-Aug-2025
A yau shirin namu da ku zai fi mayar da hankali ne a kan matakan da kasar Sin ke dauka na samun bunkasa a karkashin manufar kare muhalli, inda za mu duba wasu dabaru na sauyi da kasar ke dauka da za a yi aiki da su a sassan masana’antu. Yanzu haka kasar ta Sin ta tsara wata manufa da ta kunshi wasu ka’idoji da za a yi amfani da su wajen kawo sauye-sauyen yadda ake fitar da hayaki mai haddasa dumamar yanayi. Manufar wacce aka fitar bisa hadin gwiwa tsakanin Kwamitin Tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) da kuma Majalisar Gudanarwar Kasar Sin, ba kawai wani tsari ne na amfanin cikin gidan kasar ba, har ila yau manuniya ce ga duniya a kan yadda Sin ke matukar muhimmanta kyautata muhalli da kuma zama ja gaba a bangaren inganta yanayin doron kasa da muke rayuwa a kai.
27-Aug-2025
26-Aug-2025
Tsohon dan kwallon kafa Basine Yang Chen, ya bayyana gamsuwa game da yadda gasar kwallon kafa ta matasa ta Beijing ke kara bunkasa cikin shekaru sama da 40. Yang Chen, wanda a yanzu ke da shekaru 51, ya halarci gasar ta bana, wadda ya ce ta tuna masa yadda ya taka leda a wannan gasa sama da shekaru 40 da suka gabata.
21-Aug-2025