Kasar Sin ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasan kwallon tebur su 12, wadanda za su wakilci kasar, a gasar cin kofin nahiyar Asiya na ITTF-ATTU karo na 34, wanda za a gudanar tsakanin ranakun 19 ga zuwa 23 ga watan Fabarairu dake tafe a birnin Shenzhen, na lardin Guangdong. Tawagar ‘yan wasan ta kunshi ‘yan wasa dake matsayi na daya a duniya, wato Wang Chuqin da Sun Yingsha.
23-Jan-2025
Abubakar Haruna Bichi, dan asalin Kanon Najeriya ne, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a fannin tasirin canjin yanayi ga gandun daji, a wata jami’a mai suna NEFU dake birnin Harbin na lardin Heilongjiang a arewa maso gabashin kasar Sin. Abubakar ya bayyana yadda ya fara sabawa da rayuwa a nan kasar Sin, musamman a fannonin da suka shafi yanayi, da abinci da al’adu, da kuma ra’ayinsa kan gudummawar kasar Sin ga tinkarar matsalar sauyin yanayi a duk duniya.
21-Jan-2025
21-Jan-2025
A ’yan shekarun baya-bayan nan, kauyen Guangdong na kabilar Koriya da ke lardin Jilin na kasar Sin ya kara yin suna, har ma ya zama wani kyakkyawan katin kasuwanci na yawon bude ido na karkara na lardin. A shekarar 2010, Yang Lina, ’yar shekaru 25 da haihuwa ta koma garinsu don raya sana’a, kuma ta mayar da hankalinta kan kauyen Guangdong, tare kuma da fara sana’ar yawon shakatawa a karkara. Gidan Yang Lina yana yankin Yanbian mai cin gashin kansa na kabilar Koriya na lardin Jilin dake arewa maso gabashin kasar Sin. Ta ce, “Garin mu na Yanbian wani wuri ne mai salon musamman, yana da yanayi, da abinci, da al’adu, da ma sauran abubuwa masu halin musamman sosai na kabilar Koriya, amma a da babu wanda ya san haka.”
20-Jan-2025