03-Nov-2025
30-Oct-2025
12-Oct-2025
06-Oct-2025
06-Oct-2025
15-Sep-2025
09-Sep-2025
09-Sep-2025
Hukumar shirya gasar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta sanar da shirinta na fara bayar da lambar yabo ta zaman lafiya, karkashin taken "lambar zaman lafiya ta FIFA: Kwallon kafa na dinke duniya,". A cewar FIFA za a rika bayar da lambar ne ga mutane da suka nuna hazaka wajen wanzar da zaman lafiya, da dunkule sassan al’ummu daban daban wuri guda.
13-Nov-2025
Gwamnatin kasar Sin ta sake fito da wasu sabbin manufofi 13 domin karfafa wa jama’a kwarin gwiwar shiga a dama da su a harkokin zuba jari a kasar. A kan haka ne a farkon wannan makon, kasar Sin ta gabatar da wani tsari na matakai don inganta ci gaban zuba jari na kamfanoni ko mu ce bangarori masu zaman kansu. A bisa matakan, an yi tanadin cewa, a karkashin manyan ayyuka da suke da katamaimiyar riba a fannoni kamar layin dogo da makamashin nukiliya wadanda ke bukatar amincewa ko tabbatarwa daga sassan gwamnati da suka dace, ana goyon bayan zuba jarin kamfanoni masu zaman kansu kuma ya kamata a fayyace abubuwan da ake bukata baro-baro a fili kamar fasalin rabon hannun jarin da za a zuba, kamar yadda wata sanarwar Ofishin Babbar Majalisar Gudanarwa ta Kasar Sin ta bayyana.
12-Nov-2025
Haruna Mustapha, dan karamar hukumar Kiyawa ne daga jihar Jigawan Najeriya, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a fannin ilimin kimiyyar mutum-mutumin inji wato robot a turance a birnin Suzhou na kasar Sin. A zantawarsa da Murtala Zhang, malam Haruna ya ce duk da cewa bai dade da shigowa domin fara karatu a kasar Sin ba, amma akwai abubuwa da dama da suka burge shi a nan, inda ya bayyana ra’ayinsa kan bambancin yanayin karatu tsakanin Najeriya da kasar Sin, da yadda yake jin dadin rayuwa da karatu a nan kasar Sin.
11-Nov-2025
A garin Siqian da ke cikin gundumar Chengcheng na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin, akwai wata mace mai suna Yuan Li mai shekaru 54, wadda ’yan kauyen suke kiranta da “Shugaba Yuan”. Hakika ta taka rawar gani tun daga lokacin da ta kasance mara aikin yi a birni da komawa kauye don neman mafita a shekaru 28 da suka gabata, har zuwa jagorantar samar da gidaje 200 don noma bishiyoyin 'ya'yan itace da bude otel-otel masu zaman kansu, har ta kai ga zama “Gwarzuwar Jarumar Mata ta Kasa”, wato lambar yabo da kasar Sin take bayarwa ta musamman ga fitattun mata. Har zuwa shekara ta 2025, rayuwarta tana ci gaba da fuskantar sabbin sauye-sauye, kamar yadda bishiyoyin da aka dasa a gonarta ke ba da 'ya'yan itace kowace shekara, wadanda kullum suke cike da sabon kuzari. Hanyarta ta yin gwagwarmaya ta shaida yadda mata mazauna kauye na kasar Sin ke kokarin neman samun wadata tare karkashin tabbaci daga wajen manufofin kasar.
10-Nov-2025