10) Ban kwana—dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka
Ran 30 ga watan Mayu, 2009
Tun bayan da sabuwar kasar Sin da kasashen Afrika suka kulla huldar diplomasiya a tsakaninsu yau da shekaru wajen 60, jama'ar kasar Sin da Afirka sun hada kansu sun goyi bayan juna kuma sun tsaya tsayin daka kan ka'idoji da ra'ayoyi na yin mu'amala cikin sahihanci da yin zaman daidai wa daida da moriyar juna da hada kai da hada guiwa don samun bunkasuwa tare, ban da wannan kuma sun rika zurfafa zumunci a tsakaninsu, shi ya sa suke samun sakamako mai kyau kuma da yawan gaske.
Bunkasuwar kasar Sin tana ba da babbar gudumawa ga duk duniya. Ina iya tunawa cewa, Sin ta harba tauraron dan adam ga kasar Nijeriya, Sin ta kafa tashar gidan radiyo na FM a birnin Yamai na kasar Nijer. Wani kamfanin dake aikin shimfida layin dogo na kasar Sin ya je kasar Nijeriya domin aikin garambawul ga layukan dogo na kasar. Saboda haka kasar Sin ta kara ban sha'awa tare da burge ni sosai kuma sashen Hausa CRI ya ci a ba shi matsayi na farko na musamman na lambar yabo domin fadakarwa da kara ilmantarwa da kuma nishadantarwa.
Za mu ci gaba da sauraronku har abada tare da kara aiko muku da wasiku a kai a kai, kuma ina fata za mu ci gaba da zurfafa zumunci a tsakaninmu ba tare da gajiwa ba.
Ina kara yin fatan alheri da in kara zuwa nan kasar Sin tare da wayin kai da na samu a nan kasar Sin, kuma in tarar da dukkan ‘yan tawagar da suka yi ma jagoranci na ziyarata a kasar Sin cikin halin koshin lafiya. Amin. Ku huta lafiya.
Mohammad Idi Gargajiga