4) Ni'imtattun wurare a jihar Sichuan


Ran 28 ga watan Mayu, 2009

Idan an zabi kyawawan shahararrun ni'imtattun wuraren yawon shakatawa a duniya, to, idan an zo jihar Sichuan sai zai ji mamaki sasoi, domin jihar Sichuan jihar musamman ce a duniya da ta fi jawo hankulan dubun-dubatar mutanen kasashen duniya masu sha'awar yawon shakatawa da yin taruruwa zuwa ziyara a kasar Sin.

Mun yi ziyara ga sansanin panda na Bifengxia, to, kamar kowa ya sani, panda dabba ce mai ban sha'awa da kyawun gani tare da farin jinni a halin zamantakewar dan adam da halittu. Ina iya tunawa cewa, an taba kebe panda a matsayin alama da za ta alamanta gasar wasannin Asiya na karo na 11 da aka yi a birnin Beijing na kasar Sin. Saboda haka, panda dabba ce mai muhimmanci sosai a duniya.