5) Bikin ba da kofin kyauta a masaukin Minshan na birnin Chengdu


Ran 28 ga watan Mayu, 2009

Wannan kasaitaccen bikin ba da kofin da CRI ya yi mini ya sa na yi murna da farin ciki kwarai da gaske domin ya yi dalili na zuwata kasar Sin, saboda haka na fahimci kasar Sin sosai da sosai, kuma kyautar kofin ta kara karfafa mini guiwa tare da zaburar da ni wajen sauraron sashen Hausa na CRI. A nan ina mika babbar godiyata ga dukkan ma'aikatan sashen Hausa na CRI domin iyakacin kokarin da kuka yi na samar da ni duk irin halin da kasar Sin ke ciki a kullum da na duniya baki daya.

Ban da wannan kuma irin girmamawa da kauna da kuma kulla zumunci da aminci da na samu daga jama'ar kasar Sin na kowane yankin kasar Sin, a gaskiya ya jawo hankalina kwarai da gaske domin ya sa na ayyana a cikin zuciyata cewa, ya fi kyau in nemi aiki a sashen Hausa na CRI, saboda ina so in ba da irin tawa gudunmawa wajen kara fadakar da hausawa domin kara fahimtar kasar Sin yadda ya kamata, da kuma domin jama'ar kasar Sin da ta Afrika su kara samun kyakkyawar fahimta, to, yadda za su kara bai wa juna sakin jiki da sakin fuska a halin cudanyarsu ta zamantakewa ta yau da kullum dake tsakaninsu.