2) Ziyarata ta farko a kasar Sin
Ran 25 ga watan Mayu, 2009
Ran 25 ga watan Mayu na shekarar 2009 rana ce da na soma ziyara ga wurare daban daban a kasar Sin, domin na soma zuwa babbar ganuwa ta Badaling, wadda labarinta ya bazu a duk fadin duniya.
A gaskiya babbar ganuwar kasar Sin ta shahara sosai, kuma a yadda na fahimci babbar ganuwar kasar Sin, zan iya cewa, mutanen da suka kawo tunanin a gina wannan ganuwa dama wadanda suka yi fasalinta da kuma masu aikin gina ganuwar, dukkansu mutane ne masu karfin kishin kansu da na kasarsu.
Dalili shi ne babbar ganuwar kasar Sin an gina ta da kantagaryar dutse zalla, kuma tana da fadi da kauri sosai, kuma tana da zauruka da aka gina a tsakiyarta. Babbar ganuwa ta kasar Sin ta kawo wa jama'ar kasar Sin na wannan zamani babban abin alfahari da kuma ci gaba da samun nasara wajen ribantuwa a fannin samun kudin shiga na gwamnatin kasar Sin dangane da sha'anin yawon bude ido a kasar Sin. Domin babban abin al'ajabi ne ga kowane dan adam da ya haura kan doron ganuwar idan ya hanga ya ga yadda babbar ganuwar nan ta keta manya da kananan tsaunuka da kwazazzabe, sai dai mutum ya yi tayin sake-sake a zuciyarsa kwarai, amma ba zai iya ya gano bakin zaren ba, na yadda aka yi aka gina wannan babbar ganuwa ta kasar Sin.