An mika kyauta ga masu sauraronmu wadanda suka samu nasara a cikin gasar kacici-kacici ta kyakkyawar Sichuan
Ran 28 ga watan Mayu, 2009
A ran 27 ga wata da yamma a birnin Chengdu, hedkwatar lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, an yi bikin mika kyauta ga masu sauraronmu wadanda suka zo daga kasashe 10, kamar su Nijeriya da Amurka da Faransa da Brazil da Indiya, kuma suka samu lambar yabo ta musamman a cikin gasar kacici-kacici ta kyakkyawar Sichuan da gwamnatin lardin Sichuan da gidan rediyon kasar Sin, wato CRI suka shirya tare a duk fadin duniya tun daga ran 15 ga watan Oktoba na shekarar bara zuwa ran 15 ga watan Afrilu na bana. A cikin rabin shekara, masu sauraronmu wadanda suke zaune a yankuna da kasashe 151 na duk duniya sun fafata gasar, kuma yawan wasiku da sakwannin da suka aiko mana ya kai fiye da dubu 520.
A gun bikin mika kayan kyauta, Mr. Wang Gengnian, shugaban CRI ya bayyana cewa, a watan Mayu na shekarar bara, lardin Sichuan da ke da dimbin wuraren yawon shakatawa ya sheda bala'in girgizar kasa mai tsanani sosai. Bayan wannan bala'i daga indallahi, lardin Sichuan ya yi kokari sosai wajen farfado da sake raya sana'o'i daban daban, ciki har da sana'ar yawon shakatawa. Mr. Wang ya ce, "Bayan wannan bala'i daga indallahi mai tsanani, gidan CRI da hukumar yawon shakatawa ta lardin Sichuan sun shirya gasar kacici-kacici ta kyakkyawar Sichuan ga duk duniya domin tabbatar wa duk duniya cewa har yanzu lardin Sichuan yana da kyan gani kamar yadda yake a da. Wannan gasa ta taka rawa sosai wajen ci gaban sana'ar yawon shakatawa a lardin Sichuan."
Haka kuma a yayin bikin mika kayan kyauta, madam Huang Yanrong, mataimakiyar gwamnan lardin Sichuan ta bayyana cewa, bayan bala'in girgizar kasa, galibin muhimman wuraren yawon shakatawa na lardin Sichuan suna da kyan gani kamar yadda suke a da. Madam Huang ta kuma nuna godiya ga wadanda suke mai da hankalinsu kan lardin Sichuan. Madam Huang Yanrong ta ce, "A cikin wasiku da sakwannin da masu sauraron CRI suka aiko mana, sun kuma nuna gaisuwa da fatan alheri ga lardin Sichuan da jama'ar lardin. Yau cikin sahihanci ne, a madadin gwamnatin jama'a ta lardin da dukkan jama'armu miliyan 88, na gode da dukkan kasashen duniya da jama'a wadanda suka nuna mana goyon baya da kuma ba mu taimako ba tare da son kai ba."
Malam Mohammed Idi Gargajiga, wato shugaban kulob na masu sauraron CRI a jihar Gombe na kasar Nijeriya ya dade yana sauraren shirye-shiryen sashen Hausa na CRI. A cikin wannan gasar kacici-kacici ta kyakkyawar Sichuan, ya samu lambar yabo ta musamman, kuma yanzu yana ziyara a lardin Sichuan na kasar Sin bisa gayyatar da lardin Sichuan da CRI suka yi masa. Game da wannan gasa da ziyara, malam Gargajiga ya ce, "Na ji dadi, na yi murna da farin ciki kwarai da gaske. Bisa dalilin samun wannan sakamako a gasar kacici kacici da na yi nasara har na yi sa'ar samun damar zuwa nan kasar Sin. Wannan babban muhimmin abu ne a gare ni, ba gare ni kawai ba, har na sauran masu sauraro 'yan kulob din na Gambawa CRI's listeners's kulob, da kuma a Najeriya, ko in ce dukkan Afirka baki daya. Wannan wani karmawa ne da kasar Sin ta yi mini a karkashin jagorancin CRI. Na yi matukar farin ciki kwarai da gaske na samu lambar yabo mai matukar direja sosai daga CRI a nan kasar Sin. Ban da wannan kuma, na je wurare sassa daban daban na kasar Sin na ganewa idona. Na tabbatar da abubuwan da suke faruwa a cikin zahirin gaskiya."
Mr. Andrew Peterson wanda ya zo daga kasar Amura, kuma ya dade yana sauraran shirye-shiryen harshen Turanci na CRI ya soma yin sha'awar kasar Sin tun sai'lin yake karami. Kawo wa kasar Sin ziyara fatansa ne da ya dade yake cikin zuciyarsa. Yanzu, wannan fata ya zama gaskiya, yana jin farin ciki sosai. Mr. Andrew Peterson ya ce, "Na fi son sauraran shirye-shiryen da masu sauraro su kan iya shiga, kamar gasar kacici-kacici. Take daban daban na gasannin kacici-kacici su kan sanya mu san fannoni daban daban na kasar Sin. A shekara ta 2008, lokacin da na samu labarin cewa, CRI da hukumar yawon shakatawa ta lardin Sichuan suna yin gasar kacici-kacici ta kyakkyawar Sichuan cikin hadin gwiwa, na tuna da bala'in girgizar kasa na Wenchuan. Ina cike da tausayi ga jama'ar da suka gamu da bala'in. Na fi son samun karin bayanai game da lardin Sichuan." (Sanusi Chen)