1) Duniyarmu ta abokantaka

Ran 25 ga watan Mayu, 2009

Bisa matsayina na tsohon mai sauraron sashen Hausa na CRI har na dogon lokaci, yau da shekaru 30, ina biye da CRI sawu da kafa, kuma tare da jin dadin dukkan shirye-shiryen CRI na kullum.

Ina mika babban gaisuwata tare da fatan alheri da jinjinawa da kuma sahihiyar godiya ga jami'an CRI da dukkan ma'aikatan sashen Hausa na CRI, bisa goron gayyatar da CRI ya aiko mini domin na kawo ziyara a nan kasar Sin.

Tabbas na yi murna da farin ciki kwarai da gaske da na samu dama na zo kasar Sin, wadda tana daya daga cikin kasashen duniya da na fi sha'awar in taka kafata a cikinta ko in ziyarce ta.